Dambu

Dambu ​​abinci ne na Hausa mai daɗi da daɗi wanda aka yi da ganyen Masara, Rama da Yakuwa. Yana da sauƙin shirya.

Dambu, wani kalan abinci ne wanda ya samo asali a kasar Hausawa a tarihi. Dambu abinci ne da ba kowace mace ta iya yinshi ba, hasali ma koda mace ta kware wajen yin danbu, to fa wata rana sai ya bada ita (sai ya kiyi, wato yayi mata gardama a wani bangare) ya kan iya shaƙe mutum Musamman idan ana cin shi babu ruwa a kusa.

Dambu
Kayan haɗi Masara
Kayan haɗi Zogale
Tarihi
Asali Nijar da Najeriya
danbun nama
Danbu
Danbun Hausa a Cikin kwano

Dambu yana da farin jini a wurin dattijai har ma da samari idan su kayi marmarin shi.

Yakan haifar da ƙoshi  dan danan idan aka sanya mishi hadin ƙuli-ƙuli.

Dambu

Dambu Abincin hausawa ne da'ake yin shi da Tsakin masara ko shinkafa da Rama ko Yakuwa ko zogale ko kabeji. Ana dafawa ne ta hanyar yin Siraci.

Rabe-raben dambu

Shi dai dambu yakasu kashi kashi akwai dambun tsakin masara akwai kuma na dambun shinkafa amma wanda. Yafi tasiri a gargajiyan ce shine dambun tsakin masara wanda mafi yawan mutanen najeriya suna cinshi musamman dan arewa.[1][2]


Dambu yana da nau'i biyu

gyara sashe

Dambun tsakin masara

Dambun barjajjiyar shinkafa.

Dambun barjajjiyar alkama

Har dambun garin masara anayi yanzu. Wasu mutane su kan ci shi da mai da yaji, wasu su ci shi da miyan dage-dage.

Kayan yin dambu

gyara sashe

A nayin Dambu da tsaki (barjin inji wanda yake da laushi amma ba sosai ba) ko na masara, ko dawa, gero,har ma dana shinkafa.

Yadda ake yin dambu

gyara sashe

Dambu idan ka samu tsaki wanda aka ɓarza, da tafasa ko ganyen zogale,ko Ganye Alaiyaho,ko kuma wani nau'in ganye da muke amfani da shi, ka samu ruwa, gishiri Maggi.sai ka dora tukunya karfe a wuta ko ainahin tukunyar yin dambon sai kasaka ruwan bamasu yawa ba daga Nan sai ka kawo tukunya ta kasa wadda a kasanta fasasshe ne sai a dora ta a wannan tunkunya karfe da aka sa ruwa sai a kwaba wani abun dorawa, ko kuma duk wani abunda za'a iya amfani dashi don like tunkunya biyu. Bayan ka like su sai ka samu wani dan murfi wanda zai shiga cikin bakin tukunya kasa dinnan tunda daman nache za'a fasa kasan tunkunya, sai kasa wannan murfin yadda dai ruwan nan idan ya tafasa suracin shi zai dinga tasowa cikin tukunya kasa dinnan. Bayan kasa murfin sai ka zuba tsaki ka/ki da ka gyara shi ka/ki jika ba sosai ba kasa gishiri Maggi ganye zogale ko tafasa, sai ka sake rufewa. Bayan yayi idan ka sauke daman ka tanada man gyada soyayye sai a zuba shi roba ayi ta sakuma, kar a manta da ruwan sha ya kasance yana kusa, saboda yana shake makwogwaro.



Manazarta

gyara sashe


Manazarta

gyara sashe