Choba, Fatakwal

Yanki a birnin Fatakwal, Jihar Ribas

Choba, Port Harcourt yankin unguwa ce a birnin Fatakwal, Jihar Ribas, Najeriya.[1][2] Unguwar na da nisan 16 km (9.9 mi) daga arewa maso yamma na gundumar kasuwanci ta Port Harcourt, a gefen gabas na sabon kogin Calabar.

Choba, Fatakwal
Wuri
Map
 4°53′26″N 6°54′12″E / 4.8906°N 6.9033°E / 4.8906; 6.9033
choba market
hoton uniport

Choba asalin ƙauyen Ikwerre ne da ke ƙetaren Port Harcourt, wanda wani babban sarki ne ke tafiyar da harkokin ƙauyen a ƙauyen.[3] Sarki na yanzu shine Eze Raymond Echendu.[4] Kamar yadda Fatakwal ta faɗaɗa, Choba ta haɗe da babban birnin.[ana buƙatar hujja] Yankin China na ɗaya daga cikin gundumomin zabe 17 da ƙaramar hukumar Obio-Akpor ke gudanarwa.[5] Yawan jama'a a 1991, bisa ga ƙidayar ƙasa, ya kai 10,968, a 1996 an ƙiyasta ya ƙaru zuwa 12,980, da 27,253 a 2008.[6]

Akwai madaidaiciyar hanya wacce take kaiwa ga wani shingen bincike da zai nufi[7] wasu jahohin Najeriya kamar jihar Bayelsa da jihar Delta zuwa yamma.[8]

Choba na da nisan kilomita 466/290 daga Abuja a, babban birnin tarayyar Najeriya.[9] Jami'ar Fatakwal tana cikin Choba wanda ya hakan ya yi silar kwararowar jama'a zuwa yankin.[10]

An kafa Jami'ar Fatakwal a Choba, a shekarar 1975.[11][12] Jami'ar na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke ba da gudummawa ga tattalin arziƙin yankin da haɓakar yawan jama'ar yankin.[ana buƙatar hujja] Har wayau akwai harabar Jami'a ukku a garin, su ne; Harabar Abuja-(Abuja Campus), da Harabar Delta-(Delta Campus) da kuma Harabar Choba-(Choba Campus).[13]

Jami'ar Fatakwal na da alaƙa da Kungiyar Jami'o'in Commonwealth (ACU), Ƙungiyar Jami'o'in Afirka (AAU) da Asibitin Koyarwa na Jami'ar Fatakwal, wanda kuma yake a Choba. Jami’ar na da manyan tsofaffin ɗalibai da suka haɗa da tsohon shugaban Najeriya GCFR, Goodluck Jonathan ; Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da wasu Sanatocin Najeriya.[14]

Baya ga Jami'ar Fatakwal da Asibitin Koyarwa na Jami'ar Fatakwal, akwai dimbin makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a kusa da garin Choba Fatakwal.[15]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Choba business community embraces anti-corruption awareness". The Sun Newspaper. Retrieved 31 December 2019.
  2. "Rivers: Contender for Choba community's traditional stool dies on judgment day". Daily Post Newspaper. Retrieved 12 August 2021.
  3. Refugees, United Nations High Commissioner for. "Refworld | Nigeria: The Ikwerre Youth Association in Port Harcourt, Nigeria including their activities; treatment of their members by the authorities; negotiations with the Hillbros [Willbros]". Refworld (in Turanci). Retrieved 2022-12-15.
  4. "In Rivers, Contender For Choba Community's Traditional Stool Dies On Judgment Day". Online Nigeria. 12 August 2021. Retrieved 14 September 2022.
  5. http://wp1.inecnigeria.org/wp-content/uploads/2019/02/PU_Directory_Revised_January_2015_Rivers.pdf
  6. "Population Census In Nigeria – Nigerian Observer". nigerianobservernews.com. Retrieved 2023-04-29.
  7. "Residents flee Rivers community after cultists behead two". The guardian Newspaper. Archived from the original on 15 November 2018. Retrieved 15 September 2018.
  8. "Latest Police Attacks in Rivers state: Gunmen attack multiple police checkpoints for Rivers, kill 7 officers". BBC. Retrieved 8 May 2021.
  9. "Choba, Nigeria - Facts and information on Choba - Nigeria.Places-in-the-world.com". nigeria.places-in-the-world.com. Retrieved 2023-04-30.
  10. "University of Port Harcourt – NHEF" (in Turanci). Archived from the original on 2023-04-30. Retrieved 2023-04-30.
  11. "University of Port Harcourt Port Harcourt Nigeria". campus.africa (in Turanci). Retrieved 2023-04-29.
  12. "University of Port Harcourt Port Harcourt Nigeria". campus.africa (in Turanci). Retrieved 2023-05-02.
  13. "University of Port Harcourt". Times Higher Education (THE) (in Turanci). 2023-03-28. Retrieved 2023-04-27.
  14. "University of Port Harcourt – NHEF" (in Turanci). Archived from the original on 2023-05-04. Retrieved 2023-05-05.
  15. "The top 10 schools near Choba « SCHOOLS.HEYPLACES.COM.NG". schools.heyplaces.com.ng (in Turanci). Retrieved 2023-05-05.