Chawai ( Hausa: Fadan Chawai</link> ) wani gari ne da ke gabas da hedkwatar masarautar Tsam ta al'ummar Atsam a karamar hukumar Kauru a kudancin jihar Kaduna a yankin Middle Belt a Najeriya . Lambar gidan waya na yankin ita ce 811.

Ita ce kuma cibiyar gundumar Chawai ta Masarautar Tsam. Ita kanta masarautar da mutanenta ana kiranta Chawai.[1][2]

Filin jirgin sama na Yakubu Gowon, Jos ( IATA : JOS) shine filin jirgin sama mafi kusa da garin. Yana zaune 45.3 km kudu maso gabashin garin. Filin jirgin saman Kaduna (IATA: KAD) yana 162.7 km arewa maso yammacin garin, da filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe (IATA: ABV), 180.1 km kudu maso yammacin Chawai.

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe