Cédric Mensah (an haife shi a ranar 6 ga watan Maris din shekarar 1989) [1] ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Togo haifaffen Faransa wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasa mai tsaron gida ga ƙungiyar Stade Poitevin. Ya kasance memba a tawagar kasar Togo.

Cédric Mensah
Rayuwa
Haihuwa Marseille, 6 ga Maris, 1989 (35 shekaru)
ƙasa Faransa
Togo
Benin
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da goalkeeper coach (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Le Mans F.C. (en) Fassara-
  Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Togo2007-
Paris FC (en) Fassara2008-200920
  Olympique de Marseille (en) Fassara2010-2013240
S.R. Colmar (en) Fassara2013-201320
  Stade Lavallois (en) Fassara2018-201910
US Avranches (en) Fassara2023-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai tsaran raga
Tsayi 187 cm

Sana'a gyara sashe

An haife shi a Marseille, Mensah ya Kuma taka leda a Marseille a kulab din JS Arménienne Saint-Antoine, SA Saint-Antoine, SO Caillolais da UST Marseille. Yana da shekaru 14 ya koma FC Girondins de Bordeaux kuma a cikin kakar shekarar 2006 – 07 ya kasance a matsayin mai tsaron gida (baya) a wasa ɗaya. Ya bar Bordeaux a watan Yuli 2007, ya sanya hannu kan kwangilar OSC Lille ya buga wasa a nan a cikin ajiyar kuma a ranar 3 ga watan Agusta 2008 ya sanya hannu kan kwangila tare da Paris FC.[2] Ya buga wasanni biyu kawai a kakar wasa ta farko a Paris FC. Mai tsaron ragar ƙwallon ƙafa ya ƙare kwangilarsa da Paris FC a ranar 15 ga watan Oktoba 2009. [3] Bayan shekara guda ba tare da kulob ba ya sanya hannu kan Olympique de Marseille kuma ya taka leda tun a cikin rukunin ajiyar. [4]

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

Mensah memba ne na kungiyar kwallon kafa ta Togo,[5] ya buga wasansa na farko a Togo a ranar 1 ga watan Yuni 2008 da kungiyar kwallon kafa ta Zambia. [6]

Manazarta gyara sashe

  1. Lille OSC Profile
  2. Cédric Mensah signe au Paris FC Archived 2 May 2009 at the Wayback Machine
  3. foot-national.com (15 October 2009). "Transferts : Cédric Mensah prêt à rebondir" . Foot National (in French). Retrieved 22 May 2018.
  4. foot-national.com (12 October 2010). "Transferts : Cédric Mensah signe à Marseille" . Foot National (in French). Retrieved 22 May 2018.
  5. "FIFA-Turniere Spieler & Trainer - Cedric MENSAH" . FIFA.com (in German). Archived from the original on 18 June 2008. Retrieved 22 May 2018.
  6. Togo 1, Zambia 0 – Bad Start For World Cup 2010 In South Africa … Archived 18 July 2011 at the Wayback Machine

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe