Butholezwe Ncube (an haife shi a ranar 24 ga watan Afrilu 1992) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Zimbabwe wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya ga kungiyar AmaZulu FC da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zimbabwe.[1]
Ncube ya koma kulob din AmaZulu na Afirka ta Kudu a cikin 2016, [2] ya fara buga wasa a kulob din a ranar bude kakar wasa da Black Leopards.[3] A watan Satumba na 2018, Ncube ya rattaba hannu kan tsawaita kwantiragin shekaru uku da kulob din.[4][5]
Ncube ya fara buga wasansa na farko a duniya a ranar 24 ga watan Maris 2018 a bugun fenariti da Angola ta doke su da ci 4-2, bayan da suka tashi 2-2 a daidai lokacin da aka tashi wasa.[6]