BudgIT
BudgIT wata kungiya ce ta jama'ar Najeriya wacce ke amfani da fasaha don hulɗar 'yar ƙasa tare da haɓaka cibiyoyi don sauƙaƙe canjin zamantakewa. Kamfanin, wanda ya kaddamar da ayyuka a Legas, Najeriya, Oluseun Onigbinde da Joseph Agunbiade ne suka kafa shi a shekara ta 2011 don ba da shawarwari akan zamantakewa ta hanyar amfani da fasaha.[1]
BudgIT | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2011 |
yourbudgit.com |
Tarihi
gyara sasheShugaba Oluseun Onigbinde da Joseph Agunbiade kafa BudgIT a cikin shekara ta 2011 ta a matsayin ƙungiya yayin hackathon da aka gudanar a Co-Creation Hub. A Co-Creation Hub sun fito da ra'ayin budaddiyar isa zuwa ga data don samun damar bayanai na kudaden gwamnati don ilimin jama'a, wanda ya kai ga samar da BudgIT.[2] A cikin shekara ta 2014, Cibiyar sadarwa ta Omidyar ta saka hannun jari na $400,000 a kamfanin BudgIT.[3] A watan Yunin 2015, gwamnatin jihar Kaduna a karkashin gwamnatin Mallam El-Rufai, ta rattaba hannu a kan BudgIT don gina Budaddiyar hanyar wayar hannu ta Budget kamar Buharimeter;[4] wani dandali wanda BudgIT for Centre for Democracy and Development ya gina domin dorawa shugaba Buhari alhakin alkawurran da yayi a yakin neman zabe. A cikin Janairu 2017, BudgIT ta tara ƙarin tallafin $3 miliyan daga Omidyar Network da Bill & Melinda Gates Foundation.[5]
Tracka
gyara sasheA cikin shekara ta 2014, an ƙirƙiri Tracka don bin diddigin aiwatar da ayyukan gwamnati a cikin al'ummomi daban-daban don tabbatar da isar ayyuka.[6] Kamfanin na aiki a cikin Jihohi 20 a Najeriya, yana baiwa 'yan Najeriya damar buga hotunan ayyukan ci gaba a cikin al'ummominsu don tattaunawa da zababbun wakilansu, da kuma neman a kammala ayyukan gwamnati a yankunansu.[7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Budgit | CcHub Ventures". cchubnigeria.com. Retrieved 2019-05-24.
- ↑ Ekwealor, Victor (25 January 2017). "BudgIT raises $3 million grant from Omidyar Network and Gates Foundation". Techpoint. Retrieved 24 May 2019.
- ↑ touch, Chief Chronicler Get in (2015-07-06). "Meet Seun Onigbinde, the man whose company will turn around government transparency". Techpoint.Africa. Retrieved 2019-05-24.
- ↑ Mobile & African Tech Enthusiast │ Music │Get in touch (2015-05-05). "'Buharimeter' to hold General Muhammadu Buhari accountable". Techpoint.Africa. Retrieved 2019-05-24.
- ↑ touch, Chief Chronicler Get in (2015-06-26). "Kaduna State government signs BudgIT to build Open Budget mobile portal". Techpoint.Africa. Retrieved 2019-05-24.
- ↑ "Tracka - Track Capital Projects in your Community". tracka.ng. Retrieved 2019-05-24.
- ↑ Morley, J.M. (1994-08-17). "PFP budgit hand chain hoists". doi:10.2172/10185640.