Brian Fok ( Sinanci: 霍斌仁; an haife shi 8 ga Maris 1994) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne haifaffen Najeriya kuma ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Hong Kong wanda ke taka leda a matsayin ɗan baya a kulob din Happy Valley na farko na Hong Kong.

Brian Fok
Rayuwa
Haihuwa Jahar Kaduna, 8 ga Maris, 1994 (30 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Sir Ellis Kadoorie Secondary School (West Kowloon) (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Académico de Viseu FC (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

Rayuwar farko

gyara sashe

An haife shi a Kaduna, Najeriya ga mahaifiyar Najeriya kuma mahaifin Hong Kong, [1] Brian ya fara samun horon ƙwararrun ƙwallon ƙafa a Kwalejin ƙwallon ƙafa ta Kaduna yana ɗan shekara 5. A 2004, ya ƙaura daga Najeriya zuwa Hong Kong. Bayan ya koma Hong Kong, Brian ya horar kuma ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta matasa ta HKFC Soccer Section, Yau Tsim Mong da Hong Kong Rangers. Brian ya kammala karatunsa na sakandare a Sir Ellis Kadoorie Secondary School (West Kowloon). Brian ya kasance zakaran tseren mita 200 na tsawon shekaru 4 yana gudana a taron wasannin motsa jiki na Makarantun Hong Kong (HKSSF).

Manazarta

gyara sashe

https://www.sl10.ng/news/articles/Category/nigeria-players-abroad/shanghai-shenhua-s-hong-kong-youth-teamer-brian-fok-pledges-international-future-to-nigeria/200324