Bouli Ali Diallo (an haifeta a shekarar 1948) malamar jami'a ce kuma yar gwagwarmaya yaryar jamhuriyar Nijar.

Bouli Ali Diallo
Rayuwa
Haihuwa Nijar, 1948 (75/76 shekaru)
ƙasa Nijar
Karatu
Makaranta Université Cheikh Anta Diop (en) Fassara
Montpellier 2 University (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a Malami, gwagwarmaya da ɗan siyasa

Rayuwa da tashe gyara sashe

Ali Diallo ta halarci makarantun horo kan koyarwa da dama ciki harda makarantar horar da malamai ta Tillabéri, wadda a lokacin itace kadai mace daliba a makarantar. Daganan tawuce jami'ar Dhakar inda ta karanta Kimiyya kuma har ta samu digiri a shekarar 1978, da kuma Jami'ar kimiyya da fasaha ta Languedoc a garin Montpellier, inda ta kammala digirin digirgir a shekarar 1991.[1]

Ta dawo Nijar domin ta koyar da ilimin kimiyyar halitta a Jami'ar Abdou Moumouni University, [2] aikin da tafara tun daga shekarar 1978. Tayi aiyuka da dama, daga ciki akwai; daga shekarar 1987 zuwa shekarar 1993 tarike matsayin darakta a ma'aikatar harkokin waje, ta rike mukamin ministar ilimi ta kasa a shekarar 1995 zuwa shekarar 1996.

Ta zama mamba a hukumomin Institut de recherche pour le développement da Aide et Action sannan daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2004 ta shugabanci kungiyoyin dake fafutikar ganin an ilimantar da mata a Afrika. Tasha karbar lambobin yabo daga kasar Faransa ciki harda ta Ordre des Palmes Académiques.[1] She has remained an activist in Niger, speaking on the need to develop educational opportunities for women.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 Abdourahmane Idrissa; Samuel Decalo (1 June 2012). Historical Dictionary of Niger. Scarecrow Press. ISBN 978-0-8108-7090-1.
  2. 2.0 2.1 Alison Behnke (15 December 2007). Niger in Pictures. Twenty-First Century Books. pp. 70–. ISBN 978-0-8225-7147-6.