Bilkisu Abdullahi Shema (An haife ta ranar 28 ga Watan Yuli, shekara ta 1994) a karamar hukumar Dutsin-Ma dake a Jihar Katsina. Fitacciyar jaruma ce a masana`antar Kannywood.

Karatu gyara sashe

Ta fara karatun ta na firamari ne a makarantar Isa Kaita College of Education, bayan nan ta shiga sekandari a Government Day Secondary School Dutsin-Ma.

Fice gyara sashe

Bilkisu Shema dai na cikin mata masu tashe a fagen fina-finan Hausa a wannan lokaci. Matashiyar jarumar wadda tauraronta yake haskawa, tayi fice ne Sanadiyar wani fim ɗinta da ta fito a ciki mai suna ‘Tabbatacce Al’amari’, wannan fim shine ya sanya tayi fice a matsayi na ɗaya a cikin jaruman mata, a duniyar kannywood a wannan lokaci, domin kuwa ta baje basirarta a cikin fim ɗin a gaban shahararru `yan matan Kannywood.

Kasancewar labarin fim din kusan a kanta yake,hakan ya bata damar taka rawarta har da tsalle. Domin mafiya yawan wadanda suka kalli shirin maganar ta kawai suke yi ba ta sauran jaruman ba.

Bayan fage gyara sashe

A wata Hira, Bilkisu ta shaida cewar tun bayan da tayi fim ɗin farko, taso tayi aure domin har ta daina karbar aiki, amma Allah cikin ikonsa bai nufi yin auren ba a lokacin, duk da dai bata sanar da dalilin da ya hana yin auren ba.

Yan mata da samari na fuskantar kalu bale da yawa daga ciki da wajen masana’antar fina-finai a kokarin su na tabbatar da burin su na zama manyan taurari, amma Bilkisu tun bayan fim ɗin ‘Tabbataccen Al’amari sarki Ali Nuhu ya saka ta a wani fim.

Haka ma Ali Nuhu yayi nufin itace Wadda aka shirya zata fito a cikin fim ɗin Mansoor sai ta makara ba ta zo da wuri ba har aka canja ta da wata.

Fina-finai gyara sashe

  • Tabbatacce Al’amari
  • Sallamar so,
  • Dawood
  • Ranah. da sauransu...

Manazarta gyara sashe