Bethany Jane Mead (an haife ta a 9 May 1995) ta kasance shahararriyar 'yar wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Ingila, wadda take buga wasan gaba a ƙungiyar FA WSL na kulub din Arsenal da kuma a Ƙungiyar ƙwallon ƙafar England ta mata.

Beth Mead
Rayuwa
Haihuwa Whitby (en) Fassara, 9 Mayu 1995 (28 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Karatu
Makaranta Teesside University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Sunderland A.F.C. Women (en) Fassara2011-2017
Arsenal W.F.C. (en) Fassara2017-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Tsayi 1.63 m
hoton yar kwallo beth mead
hoton beth mead

Matakin kulub gyara sashe

Sunderland gyara sashe

Mead ta fara wasan samartakar ta ne a California Girls FC kafin ta koma kulub ɗin Middlesbrough F.C. A lokacin tana da shekara 10, sannan a shekarar da ta cika 16 ta koma kulub din Sunderland, a gasar FA Women's Premier League A kakarta ta farko a ƙungiyar ta samu cin ƙwallaye 23 a dukkanin wasannin da ta buga a gasar, kuma ta ƙare kakar ne da ƙwallaye 29 a dukkanin gasanni. Sannan a kakar da ta biyo baya ta ci ƙwallaye 30 a wasanni 28, inda ƙwallaye 15 a cikin gasar 2014 FA WSL inda ta taimaka wa kulub din Sunderland kaiwa ga gasar WSL 1. Duk da cewa Mead ta zama shahararriyar 'yar wasa bayan cigaba da kulub din Sunderland ta samu, sai ta fita don ta koma makaranta ta kammala shekaran karshenta ta jami'a. Sannan kuma ta amince da ta yi aiki a matsayin barmaid a wani pub dake garin da take, lokacin da take hutu, don nuna godiya ga masu wurin, waɗanda sun taimake ta da tallafin kuɗin da ta samu ta fara wasa.[1]

A wasan ta na farko a babban rukunin gasar, Mead ta ci ƙwallo wa Sunderland a wasan da Kulub ta ci 2–1 Liverpool wanda su ne masu riƙe nasarar fitattun zakaru.[2] A ranar 19 ga watan Yuli, 2015, Mead ta ci ƙwallaye uku hat-trick a wasanta da ƙungiyar Chelsea waɗanda su ne a saman tebur, inda ta zama mafi yawan ƙwallaye da ƙwallo takwas.[3] A cikin makon, Mead ta tsallake hatsari bayan motar ta ta yi juyi har uku sanadiyar kokarin da ta yi na kauce wa wata barewa.[4] A kuma makon da ya biyo baya, Mead ta ci ƙwallaye biyu a wasan da suka yi nasara 4–1 da Bristol, sai ƙungiyar ta ta Sunderland ta haye saman tebur din WSL 1.[5] Ta ƙare kakar 2015 na gasar WSL1 da ƙwallaye 12 a wasanni 14 kuma mafi yawan ƙwallaye a gasar.[6]

Arsenal gyara sashe

 
Beth Mead a Arsenal shekara ta 2018.

A ranar 24 ga watan Janairu, 2017, an bayyana Matan Arsenal da cewa sun sayi Mead akan wasu kuɗi da ba a bayyana ba.[7]

Manazarta gyara sashe

  1. "Mead eager to revise Canadian experience". FIFA. 19 January 2015. Archived from the original on 6 July 2015. Retrieved 2 July 2019.
  2. "Exclusive: Beth Mead". Shoot (football magazine). 23 April 2015. Archived from the original on 20 May 2015. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)
  3. Currie, Jo (19 July 2015). "Carlton Fairweather: Beth Mead 'deserves' senior England call". BBC Sport.
  4. Currie, Jo (18 July 2015). "WSL 1: Sunderland Ladies 4–0 Chelsea Ladies". BBC Sport. Retrieved 19 July 2015.
  5. "Williams says Sunderland's sights are set on the top". FA WSL. 25 July 2015.
  6. Stillman, Tim. "Arseblog Exclusive- Interview with Arsenal Women Striker Beth Mead | Arseblog News – the Arsenal news site" (in Turanci).
  7. "Beth Mead: Arsenal Ladies sign Sunderland striker ahead of WSL Spring Series". BBC Sport (in Turanci). 2017-01-24. Retrieved 2017-01-24.