Benard E. Aigbokhan malami ne ɗan ƙasar Najeriya, (an haife shi a ranar 3 ga watan Oktoba, 1951) kuma masani ne kan harkokin tattalin arziki.[1] Ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban jami'ar Samuel Adegboyega, Nigeria daga ranar 7 ga watan Janairu, 2013 zuwa ranar 6 ga watan Janairu, 2020.

Benard E. Aigbokhan
Rayuwa
Haihuwa Ewu (en) Fassara, 3 Oktoba 1952 (71 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of the West of Scotland (en) Fassara
University of Paisley (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Malami da Mai tattala arziki

Rayuwar farko gyara sashe

An haifi Eronmonsele a Ewu Ishan, Edo, Nigeria ɗa ne ga dangin David Ikhifa da Comfort Otiti Aigbokhan a ranar 3 ga watan Oktoba, 1952. A cikin shekarar 1978 ya sami digirinsa a fannin tattalin arziki a Jami'ar Gabashin London, Ingila, da Master of science a fannin tattalin arziki a Jami'ar Stirling, Scotland, 1979. PhD a fannin tattalin arziki ya zo a Jami'ar Yammacin Scotland, tsohuwar Jami'ar Paisley, Scotland, Aa shekarar 1985.[2]

Sana'a gyara sashe

Eronmonsele ya fara aikinsa ne a matsayin babban jami'i a ma'aikatar yaɗa labarai ta tarayya, jihar Legas daga shekarun 1972 zuwa 1973. Daga nan, ya tafi Scotland kuma ya yi aiki a matsayin mataimakin mai koyarwa a Jami'ar Paisley daga shekarun 1982 zuwa 1985. Bayan haka, ya dawo Najeriya ne a matsayin malami a Jami’ar Jihar Imo a shekarar 1986 sannan ya wuce Jami’ar Jihar Edo, Ekpoma, daga shekarun 1987 zuwa 1992 a matsayin mai karatu. Ya zama farfesa a fannin tattalin arziki a shekarar 1995. Daga baya ya zama ma’aikacin Resource na kwamitin UNESCO na ƙasa a jihar Legas daga shekarun 1989 zuwa 1991 da cibiyar kula da harkokin tattalin arziki da gudanar da mulki a Ibadan, Najeriya, tun daga shekarar 1991.[3]

Ayyuka gyara sashe

Eronmonsele ya yi rubutu akan Tsare-tsare, Aiki da Rarraba Kuɗi a Najeriya a cikin shekarar 1988. Ya yi rubutu akan Ka'idar Macroeconomic, Policy and Evidence a cikin shekarar 1995. Ya yi aiki a matsayin Edita na Iroro Journal of Arts and Social Sciences daga shekarun 1987 zuwa 1992. Ya kasance Mai Ba da Gudunmawa a Global visions: Beyond New World Order a shekarar 1993. Ya rubuta ayyuka 13 a cikin littattafai 23 a cikin yare 1. Ya kuma halarci tare da gabatar da kasidu a yawancin tarurrukan ilimi.[4]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Eronmonsele ya auri Fummilayo Ogedengb a ranar 3 ga watan Agusta, 1985. Sun rabu a watan Nuwamba 1988. Ya auri Rita Ekhuelohan Atoe a ranar 2 ga watan Janairu, 1991 kuma yana da 'ya'ya 3.[5]

Manazarta gyara sashe

  1. "ANEEJ mourns Board Chairman, Prof Aigbokhan". Vanguard News (in Turanci). 2020-07-14. Retrieved 2022-03-04.
  2. "SAU ORGANISES INTERNATIONAL CONFERENCE IN HONOUR OF PROFESSOR BENARD AIGBOKHAN – SAU News" (in Turanci). Archived from the original on 2022-11-28. Retrieved 2022-11-28.
  3. "Bernard Eronmonsele Aigbokhan Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2022-11-28. Retrieved 2022-11-28.
  4. "UNN Staff Profile". www.unn.edu.ng. Retrieved 2022-11-28.
  5. "UNN Staff Profile". www.unn.edu.ng. Retrieved 2022-11-28.