Ben Patterson (ɗan siyasa)
George Benjamin Patterson (An haife shi a ranar 21 ga watan Afrilun 1939) marubuci ne a Burtaniya kuma tsohon ɗan siyasa a ƙarƙashin Jam'iyyar Conservative.
Ben Patterson (ɗan siyasa) | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
25 ga Yuli, 1989 - 18 ga Yuli, 1994 District: Kent West (en) Election: 1989 European Parliament election (en)
24 ga Yuli, 1984 - 24 ga Yuli, 1989 District: Kent West (en) Election: 1984 European Parliament election (en)
17 ga Yuli, 1979 - 23 ga Yuli, 1984 District: Kent West (en) Election: 1979 European Parliament election (en) | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 21 ga Afirilu, 1939 (85 shekaru) | ||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||
Harshen uwa | Turanci | ||||||
Karatu | |||||||
Harsuna | Turanci | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Wurin aiki | City of Brussels (en) | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Conservative Party (en) |
Tarihin rayuwarsa
gyara sasheAn haifi Ben Patterson a garin Hemel Hempstead.[1] Ya fara aiki ne a matsayin malami a Kwalejin Conservative ta Swinton, yana koyar da Kasuwancin gama gari .
Fagen Siyasa
gyara sasheDaga shekarar (1968) zuwa ta (1971) ya kasance Kansila a kungiyar Hammersmith ta London.[2]
A shekara ta (1979), a farkon zaɓe na kai tsaye na Majalisar Turai, an zaɓi Patterson a matsayin ɗanmajalisa a Tarayyar Turai (MEP) don wakiltar mazabar Kent ta Yamma. Ya kasance mataimakin shugaban kwamitin tattalin arziki da harkokin kudi da manufofin masana'antu daga watan Janairun (1992) har zuwa lokacin da aka sha kaye a zaben shekarar (1994) na Turai.[1]
Jerin Litattafansa
gyara sashePatterson ya rubuta littattafai da dama, wanda suka haɗa da:[3]
- Direct Elections to the European Parliament (1974)
- Powers of the European Parliament (1979)
- Purse-Strings of Europe (1979)
- Vredeling and All That (1984)
- Europe and Employment (1984)
- VAT: The Zero Rate Issue (1988)
- European Monetary Union (1991)
- A European Currency: on track for 1999? (1994)
- Options for a Definitive VAT System (1995)
- The Co-ordination of National Fiscal Policies (1996)
- The Consequences of Abolishing Duty Free (1997)
- Adjusting to Asymmetric Shocks (1998)
- The Feasibility of a `Tobin Tax' (1999)
- The Determination of Interest Rates (1999)
- Exchange Rates and Monetary Policy (2000)
- Tax Co-ordination in the EU (2002)
- Background to the Euro (2003)
- Public Debt (2003)
- The Euro: Success or Failure? (2006)
- Understanding the Eu Budget (2011)