Bello Jibrin Gada
Bello Jibrin Gada dan siyasan Najeriya ne wanda ya taba zama Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas daga watan Mayun shekarar 1999 zuwa watan Mayu shekarar 2003. An nada shi Ministan Al'adu da Yawon Bude Ido a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2008 bayan da Shugaba Umaru 'Yar'Adua ya yi wa majalisar ministoci garambawul. Ya bar ofis a watan Maris na shekarar 2010 lokacin da Mukaddashin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa
Bello Jibrin Gada | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
17 Disamba 2008 - 17 ga Maris, 2010 ← Adetokunbo Kayode - Abubakar Sadiq Mohammed →
3 ga Yuni, 2003 -
Mayu 1999 - 2003 District: Sokoto East | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | jihar Sokoto, 1954 (69/70 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Jami'ar Bayero | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa |
Peoples Democratic Party All Nigeria Peoples Party |
Tarihi
gyara sasheAn kuma haifi Gada a shekarar 1954. Ya halarci Jami’ar Bayero ta Kano da kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. An kuma zaɓe shi Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a karkashin jam'iyyar All Nigeria People Party (ANPP), yana rike da mukami daga watan Mayu shekarar 1999 zuwa watan Mayu shekarar 2003. Ya kuma yi aiki a matsayin Mai Yaran Marasa Rinjaye a lokacin da yake kan karagar mulki. Bayan haka, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, inda kuma ya zama shugaban jam'iyyar ta Democratic Party ta jihar Sokoto.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Nigeriafirst Ng. "Bello Jibrin Gada". Archived from the original on 2010-10-29. Retrieved 2021-02-20. Cite has empty unknown parameter:
|4=
(help)CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)