Balle, Najeriya
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Balle gari ne, da ke a jihar Sokoto, a Najeriya. Kuma garin ne Hedikwatar karamar hukumar Gudu.
Balle, Najeriya | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Sokoto | |||
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Gudu | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Balle na da tazarar kilomita 36 daga garin Tangaza, da kuma kimanin kilomita 97 daga Sakkwato.
Yanki
gyara sasheBalle na a gabashin Gudu, kimanin kilomita 40 kudu maso gabas da garin Kurdula, kuma garin Karfen-Sarki yana da nisan kilomita 30 kudu maso yamma, garin Bachaka kimanin kilomita 70 daga yamma. Kasancewar ita ce hedkwatar karamar hukumar Gudu da yawa gine-ginen jama'a da na gwamnati suna cikin garin. Kamar Sakatariyar Kananan Hukumomi, Gidan Gwamna, Gidan Ma'aikata da dai sauransu.
Makarantu
gyara sasheGarin balle, yana da makarantun firamare na kwana guda uku mallaki gwamnatin jihar Sokoto, da kuma sabuwar makarantar sakandare da aka gina, ƙaramar sakandare da Model Primary School Balle.
Harshe da Ƙabila
gyara sasheMazaunan Balle sun haɗa da Hausawa da kuma Fulani, galibi ana amfani da harshen Hausa, haka nan kuma ga yaren fulbe ga wasu mazauna yankin.