Bako Sarai ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Kano wanda ya taɓa zama wakilin Dawakin Kudu/Warawa a majalisar wakilai da majalisar dokokin ƙasar. An fara zaɓen sa a shekarar 1999 kuma ya yi aiki har zuwa shekara ta 2003, sannan aka sake zaɓe a shekarar 2003 ya ci gaba da riƙe muƙaminsa har zuwa shekara ta 2007 a matsayin ɗan jam’iyyar PDP. Mustapha Dawaki Bala ne ya gaje shi a shekarar 2011. [1] [2]

Bako Sarai
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwar Sana'a

gyara sashe

An haifi Bako Sarai a watan Oktoban shekarar 1952 a jihar Kano a Najeriya. Yana riƙe da M.Sc. a fannin Injiniyanci daga Cibiyar Fasaha ta Crafield da ke Ingila. Ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Ƙaramar Hukuma a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar SDP, sannan ya kasance ɗan Majalisar Dokoki ta Ƙasa a Najeriya, inda ya yi aiki a Majalisar Wakilai daga shekarun 1999 zuwa 2003 da kuma daga shekarun 2003 zuwa 2007. [2] [3]

Aikin siyasa

gyara sashe

Bayan kammala wa'adinsa, Bako Sarai ya maye gurbin Mustapha Dawaki Bala a shekara ta 2011. [1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2025-01-04. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 "House of Representatives Member | Honourable Bako Sarai". 2007-10-20. Archived from the original on 20 October 2007. Retrieved 2025-01-04. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  3. "The House of Representatives, Federal Republic of Nigeria". 2007-12-21. Archived from the original on 21 December 2007. Retrieved 2025-01-04.