Baboucarr Njie (an haife shi a ranar 5 ga watan Yuni 1995) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Gambiya wanda a halin yanzu yake wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta USL ta Phoenix Rising FC.

Baboucarr Njie
Rayuwa
Haihuwa Serekunda (en) Fassara, 5 ga Yuni, 1995 (28 shekaru)
ƙasa Gambiya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Atlanta United 2 (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Lamban wasa 14

Sana'a gyara sashe

Njie ya buga wasan ƙwallon ƙafa na kwaleji a Kwalejin Wesleyan ta North Carolina tsawon kaka biyu a jere, ya tsallake a shekarar 2018 kuma ya dawo ƙarancin shekarunsa a cikin shekarar 2019. A lokacin da yake tare da Battling Bishops , Njie ya buga wasanni 57, inda ya zura kwallaye 34 sannan ya taimaka an zura kwallaye sau 19. [1] A lokacin kakar 2018, Njie ya taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta USL PDL tare da North Carolina FC U23, inda ya yi wasanni sau hudu.[2]

A ranar 14 ga watan Fabrairu, 2020, an sanar da cewa Njie zai rattaba hannu a kungiyar ta USL Championship Atlanta United 2.[3] Ya fara wasansa na farko a Atlanta a ranar 29 ga watan Yuli 2020, ya fara wasan tare da The Miami FC. [4]

Njie ya rattaba hannu da kungiyar Rio Grande Valley FC ta USL Championship a ranar 6 ga watan Afrilu 2021. [5]

Njie ya rattaba hannu tare da kulob ɗin Phoenix Rising FC a ranar 13 ga watan Disamba 2021. [6]

Manazarta gyara sashe

  1. "Baboucarr Njie" . N.C. Wesleyan .
  2. "North Carolina FC U23 - 2018 Regular Season - Roster - #10 - Baboucarr Njie - M/D" . www.uslleaguetwo.com .
  3. "Atlanta United 2 signs Baboucarr Njie | Atlanta United FC" .
  4. "Atlanta United 2 vs. The Miami FC - July 29, 2020 | USLChampionship.com" . www.uslchampionship.com .
  5. "Toros Bolster Squad with Arrival of Miller, Njie" . April 6, 2021.
  6. "Rising FC Signs Versatile Defender Baboucarr Njie To a Multi-Year Contract" . December 13, 2021.