Babayo Garba Gamawa

Dan siyasar Najeriya

Babayo Garba Gamawa (an haife shi a ranar 2 ga watan Fabrairun shekara ta 1966 – 14 June 2019) [1] dan kasuwa ne dan Najeriya kuma shi ne Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa a Jihar Bauchi a shekara ta 2011. Ya kasance yana da alaka da jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).[2]

Babayo Garba Gamawa
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015
District: Bauchi ta arewa
Rayuwa
Haihuwa 2 ga Faburairu, 1966
ƙasa Najeriya
Mutuwa 14 ga Yuni, 2019
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Sana'ar siyasa

gyara sashe

Babayo Garba Gamawa ya taba zama mataimakin gwamna da kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi.[3] Ya zama mataimakin gwamnan Bauchi lokacin da aka tsige Alhaji Mohammed Garba Gadi daga mukaminsa. Lokacin da aka daukaka karar wannan tsigewar kuma aka ga hukuncin da aka yanke na asali bai dace ba, Gadi ya isa ofisoshi don kwato kujerarsa. Gamawa ya ki barin kujerarsa, sai magoya bayansa suka yi bore a kan titi, suna masu cewa “Gamawa ne sahihin mataimakin gwamna”. Magoya bayan Gadi, sun yi shelar cewa "mai gida ya iso, mai riya ya nade tabarmansa." Daga karshe Gamawa zai amince kuma Gadi zai sake karɓar kujerarsa na Mataimakin Gwamna.[4][5]

A shekarar 2011, an zabe shi a matsayin Sanatan Bauchi ta Arewa mai wakiltar Majalissar Tarayya ta 7 . Ya kasance mataimakin shugaban kwamitin jiragen sama kuma memba na kwamitin sufurin kasa.

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. Senator Babayo Gamawa, former PDP deputy chairman, dies after brief illness
  2. "Babayo Garba Gamawa Homepage". Senator's Homepage.
  3. "Why I settled for Senate, by Bauchi Dep Gov". Peoples Daily. Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2022-04-04.
  4. Abubakar, Muhammad. "Nigeria: Two Deputy Governors in Bauchi". AllAfrica. Retrieved 17 May 2012.
  5. Micheal, Ishola (1 July 2010). "Bauchi: A case of two sitting deputy govs". Archived from the original on 2 June 2013. Retrieved 17 May 2012.