Augustin Nsanze
Augustin Nsanze (an haife shi a shekara ta 1953) masanin tarihi ne, ɗan siyasa kuma ɗan diflomasiyya. A halin yanzu shi ne babban mai ba da shawara ga shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza. Kafin wannan aikin Nsanze ya kasance Ministan Harkokin ƙasashen Waje na Burundi (Sakataren Harkokin Waje) daga shekarun 2009 zuwa 2011. [1] A lokacin gwamnatin shugaba Nkurunziza na farko an naɗa shi jakadan Burundi a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. [2] Kafin shiga siyasa, Nsanze farfesa ne kuma mai bincike a Jami'ar Hope Africa da Jami'ar Burundi. [3]
Augustin Nsanze | |||||
---|---|---|---|---|---|
2009 - Nuwamba, 2011 ← Antoinette Batumubwira - Laurent Kavakure (en) →
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Kibumbu (en) , 27 ga Yuli, 1953 (71 shekaru) | ||||
ƙasa | Burundi | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | University of Paris 1 Pantheon-Sorbonne (en) 1987) doctorate in France (en) : study of history (en) | ||||
Matakin karatu | doctorate (en) | ||||
Thesis director | Jean Devisse (en) | ||||
Harsuna | Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Masanin tarihi, ɗan siyasa, university teacher (en) da Mai wanzar da zaman lafiya | ||||
Employers |
Université Espoir d'Afrique (en) Jami'ar Burundi |
Manazarta
gyara sashe- ↑ Burundi from the United States Department of State
- ↑ New permanent representative of Burundi presents credentials UN.org
- ↑ Augustin Nsanze Archived 2023-04-07 at the Wayback Machine at African Studies Centre, Leiden