Antoinette Batumubwira
Antoinette Batumubwira (an haife ta a shekara ta 1956, a Ngozi, Burundi) 'yar siyasar Burundi ce. Ta kasance ministar harkokin wajen Burundi daga shekarun 2005 zuwa 2009. Tana auren tsohon ministan harkokin waje Jean-Marie Ngendahayo.
A karshen shekara ta 2007, an naɗa Batumubwira a matsayin 'yar takarar da zata gaji Alpha Oumar Konaré a matsayin shugabar hukumar Tarayyar Afirka a zaɓen wannan muƙami a farkon shekarar 2008.[1] Gwamnati ta yi kokarin samun goyon bayan wasu ƙasashen Afirka a takararta, kuma ƙasashen Afirka Great Lakes sun yi alkawarin ba ta goyon baya; sai dai daga baya gwamnati ta janye takararta tare da marawa Jean Ping na Gabon baya.[2]
Duba kuma
gyara sashe- Jerin sunayen mata na farko da suka rike mukaman siyasa a Afirka
Manazarta
gyara sashe- ↑ Jean-Pierre Nkunzimana, "Burundi seeks to join Commonwealth" Archived Nuwamba, 30, 2007 at the Wayback Machine, The New Vision, November 27, 2007.
- ↑ "Antoinette Batumubwira withdraws her candidacy for the presidency of the African Union", Burundi Réalités, February 1, 2008.