Asiya Abdullahi (chairlady) jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood tana hawa waƙoƙin soyayya tana ɗaya daga cikin jarumai mata da suka iya rawa.[1]a masana'antar.

Takaitaccen Tarihin Ta gyara sashe

Cikakken sunan ta shine Asiya Abdullahi Amma anfi sanin ta da Asiya Chairlady ko Kuma sunan da ake kiran ta dashi wato Cyleeder. An haife ta a ranar 11 ga watan Maris a shekara ta alif dari tara da casa'in da uku 1993. Tayi karatun firamare da Sakandire a garin Kano. Anyi riƙon ta a Jihar Kaduna a cikin garin Zariya. Daga baya ta dawo Jihar Kano tare da Yan uwanta. Har ta sami shiga masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud.

Masana'antar fim gyara sashe

Asiya ta shigo masana'antar a shekarar 2014 amma Bata fito a fina finai da yawa ba sedai waka. Ta iya rawa sosai shiyasa wakokin nata ke shiga sosai. Tayi wakoki da manyan jarumai kamar su Adam A Zango, Salisu S Fulani, da Kuma kananun jarumai masu tasowa.[2]

Fina finan data fito gyara sashe

  • Attajiri
  • Fansa
  • Amfanin hankali
  • Na malle
  • zaman marina
  • Murfi
  • Abubakar sadiq
  • Da sauran su

Manazarta gyara sashe

  1. https://popnable.com/nigeria/artists/59166-asiya-chairlady/biography-and-facts
  2. https://m.youtube.com/channel/UCgJeUewgso6um73PiGYneiQ