Ashley Nazira
Ashley Nazira, (an haife shi a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1995) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar, Mauritius wanda ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta San Diego Loyal SC, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙwararrun Amurka wacce ke San Diego, California, a kakar shekarar 2020 USL Championship. Tun daga 2021, yanzu yana taka leda a Saint-Pauloise FC, ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Saint-Paul, Réunion, Faransa.
Ashley Nazira | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Pamplemousses District (en) , 11 Nuwamba, 1995 (29 shekaru) | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Aikin kulob
gyara sasheNazira ya fara buga kwallon kafa tun yana shekara shida. [1] Ya, taka leda a Boulet Rouge, kulob din Premier na Mauritius, tsawon rayuwarsa har zuwa kakar 2019-2020. A lokacin da yake taka leda a kwallon kafa ta Mauritius, Nazira ya kasance dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar har sau hudu. [1]
Bayan lokacin da ya shafe a ƙasarsa,Nazira sannan ya rattaba hannu kan San Diego Loyal SC, sabuwar ƙungiyar fadada gasar USL, kan yarjejeniyar watanni 12 a cikin watan Janairu 2020. Ta yin haka, ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko na ƙasar Mauritius da ya taka leda a babban gasar a Arewacin Amirka. [2] [3]
A baya ya sami nasarar gwaji tare da kulob din Saint-Pauloise FC na Réunion Premier League a watan Fabrairun 2019 bayan ya zama babban dan wasa mai zura kwallo a raga a rukunin farko na Mauritius da kwallaye ashirin.[4] Sai dai kungiyar ta dakatar da sanya hannun a kan kudi.[5]
Shekaru biyu da rabi bayan yunƙurinsa na shiga Saint-Pauloise FC, a ƙarshe ya rattaba hannu kan ƙungiyar ta Réunionese a cikin watan Satumba 2021.
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheNazira ya fara buga wasansa na farko a duniya a Mauritius a ranar 25 ga watan Maris 2015 a wasan sada zumunci da Burundi 2-2.[6] Tare da kwallaye uku, ya kasance dan wasan da ya fi zira kwallaye a gasar cin kofin COSAFA na 2019.
Kwallayen kasa da kasa
gyara sasheAn zura kwallaye da sakamako jera kwallayen Mauritius da farko.
# | Kwanan wata | Wuri | Abokin hamayya | Ci | Sakamako | Gasa |
---|---|---|---|---|---|---|
1
|
21 ga Maris, 2019 | Churchill Park, Lautoka, Fiji | </img> New Caledonia | 3–1
|
3–1
|
Sada zumunci |
2
|
25 ga Mayu, 2019 | Filin wasa na King Zwelithini, Umlazi, Afirka ta Kudu | </img> Eswatini | 1–0
|
2–2
|
2019 COSAFA Cup |
3
|
2–1
| |||||
4
|
29 ga Mayu, 2019 | </img> Comoros | 1–1
|
1–2
| ||
5
|
18 ga Yuli, 2019 | Stade George V, Curepipe, Mauritius | </img> Seychelles | 1–0
|
1–1
|
Wasannin Tsibirin Tekun Indiya na 2019 |
6
|
22 ga Yuli, 2019 | </img> Madagascar | 1–1
|
1–1
| ||
7
|
Oktoba 13, 2019 | Estádio Nacional 12 de Julho, São Tomé, São Tomé and Principe | </img> Sao Tomé da Principe | 1–2
|
1–2
|
2021 neman cancantar shiga gasar cin kofin Afrika |
8
|
27 Maris 2022 | Anjalay Stadium, Belle Vue Harel, Mauritius | </img> Sao Tomé da Principe | 3–3
|
3–3
|
2023 cancantar shiga gasar cin kofin Afrika |
An sabunta ta ƙarshe 27 Maris 2022 |
Kididdigar kasa da kasa
gyara sashe- As of match played 13 October 2019[7]
Mauritius | |
---|---|
Shekara | Aikace-aikace |
2015 | 3 |
2016 | 0 |
2017 | 0 |
2018 | 1 |
2019 | 12 |
Jimlar | 16 |
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Pledderer, Sarah. "San Diego's Never Been Closer to Having an MLS Team" . San Diego Magazine. Retrieved 12 March 2020.Empty citation (help)
- ↑ "Football : Ashley Nazira signe au San Diego Loyal" (in French). lemauricien.com. Retrieved 12 March 2020.Empty citation (help)
- ↑ "COSAFA Cup unearths another gem as Mauritian star heads to USA" . COSAFA. Retrieved 12 March 2020.
- ↑ Gangaram, Loic. "Transfert : Ashley Nazira rejoindra la Saint-Pauloise FC en juin" (in French). Defi Media. Retrieved 12 March 2020.
- ↑ Robinson, Anthony. "Saint-Pauloise FC - AS Jeanne d'Arc : Grondin, l'habile discret" (in French). clicanoo. Retrieved 12 March 2020.
- ↑ "NFT profile" . National Football Teams. Retrieved 12 March 2020.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedNFT profile