Ashley Hartog (an haife shi a ranar 1 ga watan Satumba shekara ta 1982, a Cape Town, Western Cape ) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Afirka ta Kudu wanda ya bugawa Engen Santos ta ƙarshe . [1]

Ashley Hartog
Rayuwa
Haihuwa Cape Town, 1 Satumba 1982 (41 shekaru)
ƙasa Afirka ta kudu
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Western Province United F.C.-
Sint-Truidense V.V. (en) Fassara2007-200851
F.C. Cape Town2008-2011
SuperSport United FC2011-2011123
SuperSport United FC2011-2013438
Maritzburg United FC2013-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka

Aikin kulob gyara sashe

FC Fortune gyara sashe

Hartog ya fara aikinsa da FC Fortune, daga baya aka sanshi da Western Province United.

Lamuni ga Sint-Truidense gyara sashe

A cikin 2007, an ba shi rancen zuwa kulob din Jupiler League Sint-Truidense, inda ya buga wasanni biyar, ya zura kwallo daya.

FC Cape Town gyara sashe

Bayan shekara guda a Belgium ya koma Afirka ta Kudu, inda ya bugawa FC Cape Town . [2]

SuperSport United gyara sashe

A farkon 2011 Hartog ya koma SuperSport United a matsayin aro. Daga baya an mayar da matakin dindindin.

Maritzburg United gyara sashe

A 2013 Hartog ya koma Maritzburg United kan kwantiragin shekaru biyu. A ranar 29 ga Janairu, 2016, Maritzburg United ta sake shi, [3][4]bayan rashin jituwa tare da kocin Ernst Middendorp kan dalilan ladabtarwa tare da abokin wasan John Paintsil .[5]

Ajax Cape Town gyara sashe

A ranar 18 ga Fabrairu 2016, Hartog ya sanya hannu kan kwangilar ɗan gajeren lokaci tare da Ajax Cape Town . Bayan watanni 3 Ajax Cape Town ta sake shi.

Manazarta gyara sashe

  1. "MTN Football Page has moved". Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2012-10-14.
  2. [1][dead link]
  3. [2] Template:Failed verification
  4. "Kick off - South Africa". Archived from the original on 2007-12-22. Retrieved 2009-03-08.
  5. "Ashley Hartog · Sint-Truiden · Jupiler League (2006/07) · World Soccer Stats". Archived from the original on 2011-07-18. Retrieved 2009-03-08.