Anne Waiguru
HE Gwamna Anne Mumbi Waiguru, EGH OGW, (an haifi ta 16 ga watan Afrilu 1971) itace Gwamna ta biyu na gundumar Kirinyaga a Kenya, a ofis tun 22 ga watan Agusta 2017.
Anne Waiguru | |||||
---|---|---|---|---|---|
22 ga Augusta, 2017 -
15 Mayu 2013 - 21 Nuwamba, 2015 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 1971 (52/53 shekaru) | ||||
ƙasa | Kenya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Jami'ar Nairobi | ||||
Harsuna |
Turanci Swahili (en) Yaren Kikuyu | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Jubilee Party of Kenya (en) |
Aiki da Siyasa
gyara sasheAn zaɓe ta gwamna a zaɓukan da aka gudanar a ranar 8 ga watan Agusta 2017. A baya, tayi aiki a matsayin Sakataren Majalisar Ministoci na farko a Ma’aikatar Juyin Juya Hali da Tsare -Tsare. Shugaba Uhuru Kenyatta ne ta bada mukamin a ranar 25 ga watan Afrilu 2013, da digiri na biyu a farnin tattalin arziki daga Jami'ar Nairobi, tanada gogewa akan harkar kudi, dakuma tsarin gudanar da hada -hadar kudi, sake fasalin hidimar jama'a, a iya aiki, da gudanar da mulki. Ita ce ke bayan kafa Cibiyoyin Huduma, wuraren da 'yan Kenya za su iya samun damar ayyukan gwamnati cikin inganci, da kuma dokar siye da kashi 30%, wanda ya ba da aƙalla kashi 30 na duk kwangilolin samarwa ga gwamnati. matasa, mutane masu nakasa da mata.
Anne Waiguru ita ce ta farko a cikin mata Gwamnoni uku kacal a Kenya. Ta kasance mataimakiyar shugabar mata ta farko na Majalisar Gwamnoni a Kenya tsakanin Disamba 2017 da Janairu 2019.