Amadou Salifou
Amadou Salifou ɗan siyasan ƙasar Nijar ne wanda ya kasance Shugaban Majalisar Dokokin Nijar daga shekarata 2014 zuwa 2016.[1][2]
Rayuwa da aiki
gyara sasheSalifou Zarma ne daga yankin Yamai na Goudel. An zabe shi ga Majalisar Dokoki ta ƙasa har sau uku. Salifou ya kuma yi aiki sau biyu a matsayin shugaban majalisar Yamai.
An dakatar da Salifou daga kungiyar ci gaban al'umma ta shekarata 2013 saboda goyon bayan shugaban Nijar Mahamadou Issoufou . A ranar 24 ga Nuwamba, shekarar 2014, kwanaki huɗu bayan da Kotun Tsarin Mulki ta cire Hama Amadou daga mukaminsa na Shugaban Majalisar Ƙasa, aka zabi Salifou ya maye gurbin Amadou; ya samu kuri'u 71 daga cikin 113 daga wakilan majalisar dokokin ƙasar.
Salifou ya rasa kujerarsa a babban zaɓen shekarar 2016 . Ousseini Tinni ya maye gurbinsa a matsayin shugaban majalisar ƙasa a ranar 25 ga Maris din shekarar 2016.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Rémi Carayol (2 December 2014). "Niger : Amadou Salifou, le joker d'Issoufou" (in French). Jeune Afrique. Retrieved 18 December 2015.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Niger: Amadou Salifou élu président du Parlement" (in French). Radio France Internationale. 25 November 2014. Retrieved 18 December 2015.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Ousseini Tinni, député du PNDS, nouveau président de l'Assemblée nationale du Niger" (in French). ActuNiger. 25 March 2016. Retrieved 26 March 2016.CS1 maint: unrecognized language (link)