Alwi Shahab
‘“Alwi Shahab”’ 31 ga watan Agusta, shekara ta 1936 zuwa 17 ga watan Satumba, shekara ta alif dubu biyu da a ahırın 2020 babban ɗan jaridar ne a kasar Indonesiya sama da shekaru 40 [1] wanda ya fi mayar da hankali kan matsalolin zamantakewa da al'adu na Jakarta. [2] Ya fara aiki ne a shekarar 1960 a matsayin ɗan jarida a kamfanin dillancin labarai na Arabian Press Board a Jakarta . [3]
Alwi Shahab | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jakarta, 31 ga Augusta, 1936 |
ƙasa | Indonesiya |
Mutuwa | 17 Satumba 2020 |
Ƴan uwa | |
Ahali | Ali Shahab (en) |
Karatu | |
Harsuna | Indonesian (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida, marubuci, humanist (en) da Masanin tarihi |
Baya ga aikin jarida, Alwi ya kuma rubuta rubutun da aka tattara aƙalla cikin littattafai 11 a shekara ta alif dubu biyu da daya 2001 zuwa shekara ta alif dubu biyu da goma sha ukku 2013. Republika ce ta buga mafi yawan littattafansa, inda ya yi aiki tun shekara ta 1993. Batutuwan labaransa sun haɗa da tarihin al'adu a Jakarta . [4]
Rayuwa ta farko da iyali
gyara sasheAn haifi Alwi a Kwitang kuma shi ne ɗan fari a wajan Saleh da Salma a zuriyar Yemen. 'Yan uwansa sune Latifah, Ali Shahab da Ahmad da kuma Nur . Ya kuma kasance jikan Habib Ali bin Abdurrahman al-Habsyi na Kwitang daga jikarsa Salma, 'yar Maria Van Engels . [5]
Alwi Shahab yana da 'ya'ya shida 6 matar shi Sharifat Maryam Binti Abdullah Shahab: Yusuf Reza Shahab, Luli Mas'ad Shahab, Vera Farida Shahab, Viga Rogaya Shahab, Abdullah Shahab, da Fetty Fatimah Shahab . [6]
Ayyuka
gyara sasheYa fara aiki ne a shekarar 1960 a matsayin ɗan jarida a kamfanin dillancin labarai na Arabian Press Board a Jakarta . [7] San nana kuma a watan Agustan shekara ta 1963, ya yi aiki a kamfanin dillancin labarai na Antara . Ya yi nau'ikan ɗaukar hoto daban-daban lokacin da yake Antara, daga manema labarai na gari, 'yan sanda na majalisa, zuwa fagen tattalin arziki. Bugu da kari, na tsawon shekaru tara (1969-1978), ya kuma kasance mai ba da rahoto na fadar.[2] Alwi ya yi ritaya a Antara a shekara ta 1993, kuma daga baya ya shiga Republika.[3]
A lokacin da yake ɗan jarida, Alwi Shahab sau da yawa yana yin ɗaukar hoto a ƙasashen waje. Kamar a shekara ta 1983, ya ziyarci iyakar kasar Malaysia-Thailand yana rufe aikin don murkushe ƙungiyar Kwaminisanci ta Sojojin kasar Malaysia. [1]
Lafiya
gyara sasheAlwi Shahab yana da da ciwon sugar tun yana da shekaru 40.[8] Ya mutu a ranar 17 ga watan Satumba shekara ta alif dubu biyu da a shirin 2020 a gidansa bayan ɗan gajeren lokaci na cutar huhu. [ana buƙatar hujja][<span title="This claim needs references to reliable sources. (September 2023)">citation needed</span>]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Alwi Shahab 2007, About.
- ↑ 2.0 2.1 Ensiklopedi Jakarta 2017, Alwi Shahab.
- ↑ 3.0 3.1 Merdeka.com 2019, Profil Alwi.
- ↑ Tirto.id 2017, Alwi Shahab.
- ↑ Karta Raharja Ucu (2020-09-18). "Abah Alwi dan Kisah Tanah Betawi". Republika Online (in Harshen Indunusiya). Retrieved 2020-09-19.
- ↑ Republika Online 2013, Tahun ke-77.
- ↑ Detik.com 2017, Kenangan Tak.
- ↑ Nur Indah Farrah Audina. "BREAKING NEWS Wartawan Senior Alwi Shahab Meninggal Dunia karena Sakit Diabetes". Tribun Jakarta (in Harshen Indunusiya). Retrieved 2020-09-19.