Ali Nikzad
Ali Nikzad Persian : (an haife shine a ranar 22 ga watan satumba shekara ta 1954 )ya kasance ɗan siyasan Iran,ne kuma ɗan siyasa mai ra'ayin mazan jiya kuma tsohon minista ne a majalisar ministoci ta Kasar Iran.
Ali Nikzad | |||
---|---|---|---|
District: Ardabil, Nir, Namin and Sareyn (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ardabil (en) , 22 Satumba 1954 (70 shekaru) | ||
ƙasa | Iran | ||
Karatu | |||
Makaranta | Iran University of Science and Technology (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Shi'a |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Nikzad a shekara ta 1961. Yana da digiri na farko a ci gaban birane daga Jami'ar Elm-va-san'at (Kimiyya da Masana'antu). Sannan ya sami digiri na biyu a fannin kula da jama'a daga Jami'ar Gudanar da Masana'antu. Akbar Nikzad ɗan'uwansa ɗan siyasan Iran ne kuma tsohon Gwamnan Lardin Ardabil.
Ayyuka
gyara sasheAn nada Nikzad gwamnan lardin Ardabil a shekara ta 2005. Sannan ya kasance darektan kungiyar kananan hukumomi a ma'aikatar cikin gida har zuwa shekara ta 2009. Ya yi aiki a matsayin Ministan Sufuri da Gidaje daga watan Agusta a shekarar 2009 zuwa Yunin shekarata 2011. Ya kuma kasance mukaddashin ministan hanyoyi da sufuri daga watan Fabrairu zuwa Yunin shekara ta 2011. A matsayinsa na ministan gidaje, ya maye gurbin Mohammad Saeedikia bayan sake zaben Shugaba Mahmud Ahmadinejad.
A ranar 7 ga watan Fabrairun shekara ta 2011, Ahmadinejad ya nada Nikzad a matsayin mukaddashin ministan hanyoyi da sufuri don ya gaji tsohon korarren Minista Hamid Behbahani. An nada Nikzad a matsayin ministan kula da kayayyakin more rayuwa a watan Mayu na shekara ta 2011 lokacin da aka kirkiro ma'aikatar, inda ya hada ma'aikatun gida biyu da na birane da tituna da sufuri. A karshen shekara ta 2012, an kuma nada shi mukaddashin ministan sadarwa da fasahar kere-kere. Shugaba Ahmedinejad ya ba shi shawarar zama ministan mukamin a watan Janairun shekara ta 2013. Sai dai kuma Majalisa ba ta amince da shi ba.
Ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2013. Sai dai kuma daga baya ya ki amincewa da takararsa. A watan Yunin shekarar 2013, an zabi Nikzad a matsayin dan takarar magajin garin na Tehran. Kungiyar "Viva bazara" wacce ta kunshi kawayen Ahmedinejad ba ta iya cin zaben kananan hukumomi ba wanda kuma aka gudanar a ranar 14 ga Yunin shekara ta 2013 a matsayin zaben shugaban kasa. Saboda haka, zaɓen Nikzad a matsayin magajin garin Tehran ya zama da wuya. A zaben shekara ta 2017, an nada shi a matsayin shugaban yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa Ebrahim Raisi.[1] However, he later declined his candidacy.[2][3][4][4][5][6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Iran Election Watch 2013: Twenty four presidential candidates emerge". The International. 21 March 2013. Archived from the original on 6 June 2014. Retrieved 27 July 2013.
- ↑ "چه کسی کاندیدای نهایی دولت خواهد بود؟". IUS News. Retrieved 27 July 2013.
- ↑ "Censoring an Iranian Campaign Story". EA WorldView. 4 June 2013. Retrieved 27 July 2013.
- ↑ 4.0 4.1 "End of Ahmadinejad's "Viva Spring"". Anadolu Agency. Tehran. 17 June 2013. Retrieved 27 July 2013.
- ↑ "Ex-minister made Raisi campaign chief". 23 April 2017.
- ↑ "Is conservative Iranian candidate reviving Ahmadinejad's Cabinet?". 23 April 2017.