Ali Isyaku Danja (An haife shi a shekara ta 1962) a karamar hukumar Gezawa ta jahar Kano. ya kasance tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano a garin Ketawa. ya halarci makarantar firamare ta Yola Wangara daga shekarar 1970 – 1976, GSSS Dambatta daga shekarar 1978 – 1881.[1]

Rayuwa da Aiki

gyara sashe

Tsohon malamin makarantar firamare ɗin, ya halarci Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Kano inda ya sami Diploma, Advance Diploma da Post Graduate Diploma a ci gaban al'umma.

a fagen siyasarsa Honorabul Ali Danja an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar tarayya a jamhuriya ta uku a shekarar 1992. Daga tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2003, ya zama shugaban zartarwa na karamar hukumar Gezawa.[2] Hon. An sake zaben Danja a matsayin dan majalisar dokokin jihar Kano a shekarar 2007 – 2011 inda ya zama mai kare marasa rinjaye a majalisar. An sake zabe shi a wannan kujera a shekarar 2011 – 2015 kuma ya zama mataimakin shugaban majalisar daga bisani ya zama shugaban majalisar. Ankara zabar Honorabul Isyaku Ali Danja a karo na uku a matsayin dan majalisar dokokin jihar Kano a shekarar 2015, har wayau, Hakama an kara zaɓar shi a Karo na hudu a shekarar 2019-2023.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.lindaikejisblog.com/2020/2/former-kano-assembly-speaker-isyaku-ali-danja-arrested-by-efcc.html[permanent dead link]
  2. https://dalafmkano.com/?p=2535