Alan Paton
Alan Stewart Paton (11 ga watan Janairun 1903 - 12 ga watan Afrilu 1988) marubuci ne na Afirka ta Kudu kuma mai fafutukar yaki da wariyar launin fata. Rubuce-Rubucensa sun haɗa da litattafan Cry, The Beloved Country, Too Late the Phalarope da wakar nan mai suna The Wasteland .
Alan Paton | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Pietermaritzburg (en) , 11 ga Janairu, 1903 |
ƙasa | Afirka ta kudu |
Mutuwa | Durban, 12 ga Afirilu, 1988 |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Natal |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, autobiographer (en) , marubin wasannin kwaykwayo da ɗan siyasa |
Muhimman ayyuka | Cry, the Beloved Country (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Artistic movement | novella (en) |
Imani | |
Addini | Anglicanism (en) |
Jam'iyar siyasa | Liberal Party of South Africa (en) |
IMDb | nm0665704 |
Iyali
gyara sasheAn haifi Paton a Pietermaritzburg dake a cikin garin Colony na Natal (yanzu yankin KwaZulu-Natal na Afirka ta Kudu), ɗan ma'aikacin gwamnati (wanda yayi imani da Christadelphian). Bayan ya halarci Kwalejin Maritzburg, ya samu digiri na farko na Kimiyya a Jami'ar Natal a garinsu, sannan ya sami difloma. Bayan kammala karatunsa, Paton ya yi aiki a matsayin malami, na farko a Makarantar Sakandare ta Ixopo, sannan daga baya ya koma Kwalejin Maritzburg . Yayinda yake a Ixopo ya hadu da Dorrie Francis Lusted . Sun yi aure a 1928 kuma sun kasance tare har zuwa mutuwarta q emphysema a 1967.