Al'ummar Musulmin Indiya hukuma ce ta musulmai a Indiya. Hakanan an yarda da ita azaman babbar ƙungiyar wakilai ta Musulmai a ƙasar. Hedikwatar al'umma tana cikin Daryaganj, New Delhi . Grand Mufti na Indiya shine Shugaban wannan Hukuma. Sheikh Abubakar Ahmad a yanzu haka yana matsayin Shugaba tun daga shekarar alif dubu biyu da goma sha tara 2019. An yiwa hukumar rijista a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin 1954 kuma tana aiki da hukumomin kasa guda tara a karkashin hukumar.