Ajwad bin Zamil
Ajwad bin Zamil bin Saif Al-Uqaili (1418 - 1496 Miladiyya) sarki ne wanda ya mulki kasashen gabashin tsbirin larabawa da ya hada da Ahsa' da Bahren. Yayi mulki ne karkashin daular da aka fi sani da "Al-imarah Al-Jabriyya".[1]
Ajwad bin Zamil | |||
---|---|---|---|
1470 - 1496 ← Q125676769 - Q125604936 → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Al-Ahsa City (en) , 1418 | ||
ƙasa | Jabrids (en) | ||
Harshen uwa | Larabci | ||
Mutuwa | unknown value, 1505 | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Q125678759 | ||
Yara | |||
Ahali | Q125676769 | ||
Ƴan uwa |
view
| ||
Karatu | |||
Harsuna | Larabci | ||
Sana'a | |||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Nasabarshi
gyara sasheSunanshi Ajwad bin Zamil bin Saif Al-Uqaili Al-jabri. Ya shahara ne da sunan Ibn Jabr (Dan Jabr) saboda sunan kakanshi. Kuma dan asalin yankin Najd ne tare da kuma kasancewa akan mazjabar malikiyya.
An haife shi a garin Alhasa a watan Ramadan shekara ta 1418 Miladiyya.[2]
Rayuwarshi
gyara sasheSultan Ajwad bin Zamil al-Jabri ya kasance mai addini, kuma yana da dabi'ar karantar fikihu. Hakan yasa ya jajirce wajen gudanar da ayyukan addinin Musulunci, kamar sallar Juma'a da halartar jam'i, kuma ya yi aikin Hajji fiye da sau daya.
Siffofinsa
gyara sasheYawancin littafan da suka yi bayani akan rayuwar Sarki Ajwad suna nune cewa ya kasance mutum ne mai kyawawan dabi'u. Sannan ya shahara a fagen hawan doki da yawan kyauta.
Wasu manazarta sun bayyana shi a matsayin daya daga cikin shahararrun sarakunan da suka yi suna, wadanda suka bambanta da karamci, da kyawawan halaye, irin na Larabawa wanda ke iya ba da abin da suke da shi da abin da suka mallaka don girmama bako, da ba shi hakkinsa, wanda hakan nema yasa suka zama abin koyi a wajen karamci. Haka nan Sarki Ajwad ya yi fice wajen hakuri, da juriya akan abinda ya shafi mazhaba a addini, watakila abin da ke tabbatar da haka shi ne, ya yi kuma amfani da wasu malaman fikihu Ahlus-Sunnah bayan sun kasance ya Shi’a. Da yake Sarkin Ajwad ya kasance mafificin masu iya hawan dawaki, ya jajirce wajen yaki. Marubutan tarihi sun shaida cewa wannan sarkin yana da halaye masu kyawun gaske.
Hawansa Mulki
gyara sasheManazarta sun yi ssabani akan sherar da sarki Ajwad ya hau karagar mulki. Hakan yasa wasu daga cikin su suka fi karkata kan cewa ya hau mulki ne a shekara ta 875 (Hijriyya) wanda yayi daidai da shekarar 1470 miladiyya.
Masarautarsa ta kasance a farkon karni na goma, kamar yadda ta kasance a ƙauyen Al-Manizla, a cikin Al-Ahsa a yau, kuma fadarsa tana yamma da ƙauyen da ake da su har zuwa yanzu.
A shekara ta 912 bayan hijira Ibn Zamil ya yi hajjin taron fiye da dubu talatin.
Mutuwa
gyara sasheSarki Ajwad bin Zamil ya rasu a shekara ta 1496 M, sannan dan cikinsa Muhammad shi ya gaje shi.