Shugabanci
Shugabanci ko 'Jagoranci yana nufin shugabantar al'ummah ko mulki ko samun madafan iko ko jagorancin al’umma. Haka kuma shugaba shi ke tabbatar da cewa an bin doka da oda kamar yadda aka tsara. Kuma shi ne mai bayar da umarni wajen tafiyar da ayyukkan yau da kullum wadanda mabiyansa ne sukeyi. Shi ko wucewa gaban al’ummarsa na biye da shi. Kowa ya zura masa ido don daukan umarni da biyayya ga abin da ake so ya yi a bisa tsarin doka. Duk da cewa shugaba idan ya taka doka za'a iya hukuntashi[1] Abin lura a nan shi ne shugaba bawa ne wajen hidimta wa al’ummarsa, ta hanyar jagorantar su a cikin al’amauran da ya shafi cigaban su da Kuma Abubuwan bukatunsu. Jagoranci muhimmin aiki ne na gudanarwa wanda ke taimakawa wajen haɓaka aiki da kuma cimma burin Al'umma.[2]
Wasu Abubuwan da suke wajibi ga shugaba yayiwa alu'umma
gyara sashe- Ilimi: Dole ne shugaba na-gari ya zama yana da ilimin da zai gudanar da aikinsa, hakan zai sa mabiya bayan sa su girmama shi tare da amincewa da duk wani hukunci da zai yanke.
- Gaskiya da tsare mutuncin kai: Dole ne shugaba ya zama mai tsananin gaskiya, ya kamata na kasa da shi su iya bada shaidar Shuganbansu a matsayin mai gaskiya, ba wai game da aiki kawai ba har ma akan irin halayen sa. Shugaba na gari shi ne wanda ba ya aikata abubuwan da suka bijirewa yardar da aka yi masa a wurin aiki da kuma a sunan sa.
- Yarda da kai: Dole ne shugaba nagari ya zama mutumin da ya yarda da kansa wajen fuskantar kowace irin matsala da za ta iya tasowa, duk kuwa irin wahalar da ke tattare da ita da kuma faxuwar gaba. Lallai ne ya nuna waxannan halaye ta yadda jama’a za su gani a cikin ayyukan shi da kuma halayen shi.
- Qarfin tunkarar aiki da kuma neman nasara akai: Dole ne shugaba ya yi imani da aikin da yake yi. Da wannan ne zai ji daxin muqamin shi ya kuma girmama shi sannan kuma ya samu qwarin gwiwar gudanar da manufofin da ya sa a gaba.
- Bayyana aikace-aikacensa: Wannan na nufin ya kamata shugaban kirki ya iya bayani ko bada rahoton aikace-aikacensa. Yana da muhimmanci ga shugaba ya samar da isassun bayanai ga na qasa da shi a game da aikace-aikacen qungiyar da kuma wuraren da aka samu matsaloli da kuma nasarorin da aka samu.
- Jajircewa: Dole ne shugaba na gari ya zamo mai jajircewa a kowane irin yanayi, kada ya karaya har sai ya kai ga samun nasara. Shugaba na gari shine wanda: BA YA GAZAWA
- Mai qirqira: Ba ya tsayawa jiran wai sai mabiyan sa sun yi abu, sai dai kawai ayi kwatance da shi, ta yadda da ya kawo sabon tsari sai mabiya su karva hannu bi-biyu. wannan shine zai kawo ci gaba da samun nasara.
- Sanin makamar hulxa da jama’a: Dole ne shugaba ya kyautata alaqar sa da al’umar da suke tare da shi da kuma na waje,sannan kuma ya zamo mai la’akari da ra’ayoyin mabiyan sa.
- Ladabtarwa da kyautatawa: Dole ne shugaba na kirki ya zama zai iya ladabtar da masu laifi, ya kuma sakawa waxanda su ka yi aiki tuquru, ma’ana waxanda suka yi abin kirki.
- Mutuntawa: daya daga cikin alamun shugaba na gari shi ne mutunta na qasa da shi, kuma idan ka mutunta wasu, kai ma za a mutunta ka. Idan shugaba ya gaza mutunta [3] mabiyanshi, to lallai zai yi wahala a gare shi su mutunta shi. Akan ce dukkan wanda ka ga ana mutunta shi, to shi ma ya mutunta kan shi ne. A wasu lokuta mukan ba da umarni ne kawai mu manta da mutuntaka, bayan kowa na da irin na shi ra’ayin kuma shima ya na so ace yana ba da umarni, duk kuwa da irin matsayin shi. Saboda har sai mun mutunta sauran jama’a irin yadda muke so a mutunta mu kafin mu ma a mutunta mun.
- Adalici ka kowa: adalci wa kowa batare da nuna kabilanci ko fifiko ba ko nuna bangarenci ko alfarma sabida addini ko al`ada.