Aïssatou Cissé ko Aissatou Cisse (an haife ta a shekara ta 1970/1) marubuciyar ce a Senegal mai nakasa wanda tazama mai ba da shawara ga Shugaban Senegal.

Aisasatou Cissé
Rayuwa
Haihuwa Dakar (en) Fassara, 1971 (52/53 shekaru)
ƙasa Senegal
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a marubuci

An haifi Cissé a Niayes Thioker a cikin Dakar kusan shekarn 1971. Mahaifiyarta tana da rheumatism kuma a lokacin haihuwa Cissé hannayensa da ƙafafunsa sun rabu da mutanen da ke taimakon haihuwa. Wannan ya bar Cissé da nakasa na dindindin.Ta samu nasarori da dama tare da goyon bayan iyayenta. [1]

Cissé tazama marubuciya mai nasara. Ta rubuta littafinta na farko Zeina a cikin shekaran 2002 da Linguère Fatim bayan shekaru biyu. Ta samu lambar yabo a kasar Libiya. [2]

Ta yi rubutu game da rashin adalcin wata yarinya 'yar Senegal da aka tura gidan yari saboda ta zubar da cikin ba bisa ka'ida ba. Hakan ya faru ne duk da raguwar cikin da aka samu sakamakon fyaden da aka yi mata tana shekara goma sha uku. [1]

An nada Cissé a matsayin mai ba da shawara na musamman ga shugaban Senegal Macky Sal.[1] Ta yi aiki tare da Ministan Lafiya da Ayyukan Jama'a don inganta wuraren wasanni na kasar don masu nakasa. Ta taimaka da ƙungiyar Senagalese mai suna ASEDEME. ASEDEME kungiya ce ta taimakon kai da aka fara a shekaran 1989 don taimakawa yara hamsin 50 masu matsalar koyo don samun ilimi. [3]

  1. 1.0 1.1 1.2 Portrait Aissatou Cisse, January 2014, Xibar.net, Retrieved 3 April 2016
  2. Aissatou Cisse, Handicapped writer, 2011, Leral.net, in French, Retrieved 2 April 2016
  3. ASEDEME, Retrieved 3 April 2016