Ahmad Muhammad Bawa ( an haife shi a ranar 1 ga watan Janairun, shekara ta alif ɗari tara da arba'in da uku1943) Miladiyya.malami ne ɗan Najeriya kuma ɗan siyasa daga Faskari, Jihar Katsina. Bawa ya rike manyan mukaman gwamnati da dama, ya kasance kwamishinan ilimi da ayyuka na musamman na Jihar Katsina (daga shekarar alif 1988 zuwa shekarar alif 1989)[1] Daga baya aka tura shi ofishin gwamnati a matsayin Darakta Janar daga shekarar alif 1989 zuwa shekarar alif 1991; Ya kasance Ciyaman na Karamar Hukumar Faskari daga shekara ta alif 1994 zuwa shekara ta alif 1996. A watan Janairun shekarar alif 1998 aka nada shi ma’aikacin dindindin na hukumar daukar ma’aikata ta Jihar Katsina, matsayin da ya rike har tsawon shekaru 8.[2]

Ahmad Muhammad Bawa
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
takadda akan ahmad muhammad

Bawa ya fara karatunsa da makarantar Islamiyya a gida, daga baya ya tafi makarantar firamare ta Faskari daga shekara ta alif 1952 zuwa shekarar alif 1955; daga shekara ta alif 1956 zuwa shekarar alif 1958, ya kasance a Senior Primary School Dutsinma dake Funtua. Daga watan Janairu, shekara ta alif 1959 zuwa watan Disamba, shekarar alif 1960, ya kasance dalibi a makarantar Katsina Teachers College don samun takardar shedar koyarwa ta Grade III, sannan daga shekara ta alif 1962 zuwa shekarar alif 1963, ya koma wannan kwalejin don samun takardar shaidar digiri na biyu na malamai. A shekara ta alif 1965, Bawa ya tafi Kwalejin Horar da Malamai ta Kano domin shaidar karatun ilimin koyarwa ta kasa, kuma ya kammala a shekara ta alif 1968. Yayin da a watan Satumba, shekara ta alif 1972, ya samu shiga jami'ar ABU Zaria domin yin karatun digiri na farko. Ya sauke karatu a shekarar alif 1975.[2]

Kasancewar Bawa kwararren malami, ya fara koyarwa a shekarar alif 1961, a makarantar firamare, inda ya kai matsayin shugaban makarantar a shekara ta alif 1964. Ya kuma koyar a makarantar sakandare ta Zariya (Alhuda-huda) da Kwalejin Barewa da kuma Kwalejin Malamai ta Mani UPE. Daga baya aka tura shi sashin Inspectorate na ma’aikatar ilimi ta jihar. Bayan kammala karatunsa na Jami’ar ABU A shekara ta alif 1975, ya yi koyarwa na wani dan lokaci a Kwalejin Malamai ta Katsina, inda kuma ya nada Shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati Daura (a watan Nuwamba, shekara ta alif 1975 zuwa watan Satumba, shekara ta alif 1979), da Kwalejin Gwamnati Katsina (daga watan Satumba, shekara ta alif 1979, zuwa watan Satumba, shekarar alif 1982). An kara masa girma zuwa matsayin Zonal Inspector of Education na shiyyar Malumfashi sannan daga watan Oktoba, shekara ta alif 1983, zuwa watan Agusta, shekara ta alif 1984, Mataimakin Darakta a Hedikwatar Ilimi ta Kaduna. Daga shekara ta alif 1984 zuwa shekarar alif 1987, ya kasance shugaban karamar hukumar Kankia tilo. A shekarar alif 1987, ya samu mukamin sakatare na dindindin, wanda ya rike na tsawon shekaru biyu (shekarar alif 1987 zuwa shekarar alif 1988). An nada shi kwamishinan ilimi da ayyuka na musamman na jihar Katsina wanda ya rike na tsawon shekaru biyu (daga shekara ta alif 1988 zuwa shekarar alif 1989). An tura shi ofishin Gwamna a [3]matsayin Darakta Janar daga shekara ta alif 1989 zuwa shekara ta alif 1991. Ya yi ritaya daga aiki a watan Afrilun, shekara ta alif 1991.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.shineyoureye.org/person/ahmed-bawa-kuka
  2. 2.0 2.1 2.2 Muhammad Bawa, Garba (1993). Katsina State Pictorial and Historical Sketches. Katsina: Katsina State Historical Sketches. pp. 21–24. ISBN 9789789394890.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-13. Retrieved 2023-07-13.