Adam Abdullahi Adam
Adam Abdullahi Adam wanda a kafi sani da (Daddy hikima ko kuma Abale) jarumi ne a masana'antar shirya fina-finan Hausa (kannywood) yana daga cikin jarumai da yanzu tauraran su ke haskawa a masana'antar ya fito a jerin shirye-shirye masu yawa wanda hakan yabashi farin jini a arewacin Najeriya Shirin da yafi daukaka daga cikin shirye-shiryen daya fito sune kamar haka ana masa inkiya da Abale,sanda,rojo Sanda, A Duniya da dai sauransu.[1]
Rayuwar farko da Ilimi
gyara sasheDaddy Hikima, An haifeshi a ranar 16 ga watan maris shekarar dubu daya da dari Tara da tsassa,in da daya miladiyya 1991 a jihar kano ta Najeriya, wanda a yanzu ya nada shekaru 32 a duniya. Ya fara karatu duk a jihar Kano, inda yayi firamarinsa, sannan ya wuce makarantar sakandiri duk a Kano, daga nan ne ya tafi makarantar koyon jinya da unguwarzoma. Daddy hikima ya shiga harkan fina-finan hausa a shekarar 2020 inda ya shahara bayan ya fito a wani shiri mai dogon zango wanda ake kira da A duniya wanda tijjani asase ya shirya.
Wasu daga cikin fina-finansa
gyara sashe- A duniya
- Sanda
- Haram
- Uku sau Uku
- Labarina
- Asin da Asin
- Farin wata
- Yan zamani
- Na ladidi
- Makaryata
iyali
gyara sasheyayi aure a 27 ga watan junairun shekarar 2023 a karamar hukumar kumbotso.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Daga Bakin Mai Ita tare da Daddy Hikima". BBC Hausa.Com. 31 August 2023. Retrieved 7 October 2023.
- ↑ Khalid, Aisha (24 January 2023). "Jarumi Abale Zai Angwance, Katin Auren da Hoton Kyakyawar Amaryarsa Sun Fito". legit.hausa.ng. Retrieved 7 October 2023.