Abu Bakar bin Suleiman (an haife shi a ranar 4 ga watan Fabrairu shekarata 1944) [1] likitan Malaysia ne, mai kula da ilimi, babban jami'in kasuwanci kuma tsohon ma'aikacin gwamnati. A yanzu haka shine ne shugaban IHH Healthcare, babbar kungiyar kiwon lafiya mai zaman kanta ta Asiya, kuma shugaban IMU Group, mahaifin kamfanin na International Medical University a Kuala Lumpur . Ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban jami’a (shugaban) Jami’ar Likita ta Duniya daga shekarar 2001 zuwa shekara ta 2015. [2]

Abu Bakar Bin Sulaiman
Rayuwa
Haihuwa Johor Bahru (en) Fassara, 1944 (79/80 shekaru)
ƙasa Maleziya
Sana'a
Sana'a likita
Mamba Fellow of the Royal College of Surgeons of Edinburgh (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci

Daga shekarar 1991 zuwa shekara ta 2001, Abu Bakar ya kasance Darakta-Janar na Lafiya a Ma'aikatar Lafiya ta Malaysia . Shi shugaban wasu rukunin kungiyoyin likitocin kasar ne, gami da Kungiyar Informatics ta Lafiya ta Malaysia, Gidauniyar Kidney ta Kasa da kuma Asibitocin Asibitoci Masu zaman kansu na Malaysia. [3]

Abu Bakar yana da Digiri na Likitanci da kuma Likita na Tiyata a Jami'ar Monash, inda ya kammala karatun a shekarar 1968 Abu Bakar ya taba zama shugaban kungiyar likitocin Malaysia a shekarar (1986-1987). [4] [5]

Manazarta

gyara sashe
  1. Faridah Abdul Rashid (2012). Research on the early Malay doctors 1900-1957, Malaya and Singapore. Australia: Xlibris Corporation. p. 279. ISBN 978-1-4691-7244-6. OCLC 822073131.
  2. "Principal Officers". IMU.
  3. "Abu Bakar Suleiman". Prominent Monash Alumnus. Monash University. Archived from the original on 5 May 2008. Retrieved 2008-05-14.
  4. Prominent Alumni: Tan Sri Dato' Dr Abu Bakar Suleiman Archived ga Maris, 23, 2014 at the Wayback Machine, Monash University
  5. Abu Bakar bin Suleiman M.D., Bloomberg
  6. Empty citation (help)