Abdul Qahar Khan Wadan ( Pashto ), ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan, daga watan Agustan shekarar alif dubu biyu da goma sha ukku 2013 zuwa watan Mayun shekarar alif dubu biyu da goma sha takwas 2018.

Abdul Qahar Wadan
Member of the 14th National Assembly of Pakistan (en) Fassara

30 ga Augusta, 2013 -
District: NA-263 Kila Abdullah (en) Fassara
Member of the National Assembly of Pakistan (en) Fassara

Rayuwa
ƙasa Pakistan
Harshen uwa Urdu
Karatu
Harsuna Urdu
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Pashtunkhwa Milli Awami Party (en) Fassara

Harkokin siyasa

gyara sashe

Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Balochistan a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Pakhtun-khwa Milli Awami Party (PKMAP) daga Mazaɓar PB-12 (Qilla Abdullah-II) a babban zaɓen Pakistan na shekarar alif dubu biyu da goma sha ukku 2013 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u dubu biyar da dari takwas da ashirin da biyu 5,822 kuma ya rasa kujerar a hannun Zmrak Khan .[1]

An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ɗan takarar PKMAP daga Mazaɓar NA- dari biyu da sittin da biyu 262 (Killa Abdullah) a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a watan Agustan shekarar alif dubu biyu da goma sha uku 2013.[2][3] Kujerar ta zama babu kowa ne bayan Mehmood Khan Achakzai wanda ya lashe zaɓen a watan Mayun shekarar alif dubu biyu da goma sha uku 2013 ya bar kujerar domin ci gaba da riƙe kujerar da ya samu a Mazaɓarsa majalisar dokokin ƙasar.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 7 April 2018.
  2. "By-elections spring some upsets". DAWN.COM (in Turanci). 23 August 2013. Archived from the original on 5 March 2017. Retrieved 6 March 2017.
  3. "PML-N, PkMAP emerge victorious in Balochistan". The Nation. Archived from the original on 7 March 2017. Retrieved 6 March 2017.
  4. "Mehmood Khan Achakzai leading in two NA seats". DAWN.COM (in Turanci). 11 May 2013. Archived from the original on 10 April 2017. Retrieved 9 April 2017.