Abdul Aziz Yusif (An haife shine a shekara ta 10 ga watan Nuwamba shekarata alip 1991) a Ghana sana'ar sa ƙwallon kafa yana taka Leda a matsayin winger yana wasan sa a kungiyar Budaiyya Club a Bahrain.[1]

Abdul Aziz Yusif
Rayuwa
Haihuwa Ghana, 10 Nuwamba, 1991 (32 shekaru)
ƙasa Ghana
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Asante Kotoko F.C. (en) Fassara2012-2015
Smouha SC (en) Fassara2015-2015141
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Abdul_Aziz_Yusif_

Ayyuka gyara sashe

Farkon aiki gyara sashe

Yusif ya fara aikinsa ne da Royal Knights FC, kafin ya koma kulob din Real Tamale United a tsakanin shekarar 2009-zuwa 2010 Glo Ghana Premier League .

Kotoko gyara sashe

A ranar 9 ga watan Janairun shekara ta 2013, Yusif ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu tare da ƙungiyar Firimiya ta kasar Ghana Asante Kotoko bayan ya yi rawar gani a farkon wasanninsa na farko a Real Tamale United .

Smouha gyara sashe

A ranar 5 ga watan Agusta na shekara ta 2014, Yusif ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku tare da ƙattai na Masar Smouha SC a kan musayar kyauta. Ya ci ƙwallonsa ta farko a wasan sada zumunci da suka doke Al Teram FC da ci 3-2 a ranar 20 ga watan Agusta na shekara ta 2014.

AC Tripoli gyara sashe

A ranar 1 ga watan Satumba na shekara ta 2015, Yusif ya koma ƙungiyar AC Tripoli ta Premier League a kwantiragin shekaru biyu.[2][3]

Kungiyar Al Shabab gyara sashe

Bayan kusan kwallaye 15 a hukumance ga AC Tripoli,Abdul Aziz ya koma kungiyar Al-Shabab ta gasar Premier ta Bahraini .

AC Tripoli gyara sashe

Bayan wani lokaci a ƙungiyar AL Shabab,Abdul Aziz ya koma AC Tripoli a ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2018.

A ranar 7 ga watan Mayu na shekarar ta 2015 aka sanar da cewa zai yi gwaji tare da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta New League Red Bulls .

Ƙungiyar Budaiya gyara sashe

A watan Janairun na shekara ta 2020, Yusif ya koma Bahrain ya koma Budaiya Club . [4]

Girmamawa ta Mutum gyara sashe

Real Tamale United
  • Na Biyu Wanda Ya Fi Bada Ƙwallaye a Gasar Premier ta shekarar 2010 zuwa Ghana

Manazarta gyara sashe

  1. Post on Abdul Aziz Yusif' official Instagram account, instagram.com, 20 January 2020
  2. "Yusif discloses reasons behind his move to AC Tripoli". ghanaweb.com. Retrieved 2019-05-01.
  3. "AC Tripoli striker Yusif eyes more goals in Lebanon". goal.com. Retrieved 2019-05-01.
  4. Post on Abdul Aziz Yusif' official Instagram account, instagram.com, 20 January 2020