Abdoul Moubarak Aïgba
Dan wasan kwallon kafa a Togo
Abdoul Moubarak Aïgba (an haife shi ranar 5 ga watan Agusta 1997) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Togo wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasa mai tsaron ragar kulob ɗin Sofapaka da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Togo.
Abdoul Moubarak Aïgba | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Togo |
Suna | Abdoul (mul) |
Shekarun haihuwa | 5 ga Augusta, 1997 |
Wurin haihuwa | Kara (en) |
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa |
Wasa | ƙwallon ƙafa |
Sana'a
gyara sasheAïgba ya fara aikinsa da kungiyar Ifodje Atakpamé ta Togo, kafin ya koma AS Douanes a shekarar 2016. Bayan dogon tarihin canja wuri, ya koma kulob din Sofapaka na Kenya a cikin watan Maris 2021.[1]
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheAïgba ya fara buga wasansa na farko tare da tawagar kasar Togo a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Afrika 0-0 2020 da Benin a ranar 28 ga watan Yuli 2021.[2]
Manazarta
gyara sasheHanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Abdoul Moubarak Aïgba at National-Football-Teams.com
- Sofapaka Profile Archived 2023-04-07 at the Wayback Machine