Abdin Mohamed Ali Salih FAAS FTWAS FIWRA (Larabci: عابدين محمد علي صالح‎, an haife shi a shekara ta (1944)[1] farfesa ne a fannin injiniyanci (civil engineering) na kasar Sudan a Jami'ar Khartoum kuma kwararre kan albarkatun ruwa na UNESCO.[2] [3]

Abdin Mohamed Ali Salih
Rayuwa
Haihuwa Wad Madani (en) Fassara, 1 ga Janairu, 1944 (80 shekaru)
ƙasa Sudan
Karatu
Makaranta University of Padua (en) Fassara diploma (en) Fassara
Imperial College London (en) Fassara Doctor of Philosophy (en) Fassara
Jami'ar Khartoum
(1963 - 1969) Digiri a kimiyya
Matakin karatu doctorate (en) Fassara
Doctor of Philosophy (en) Fassara
diploma (en) Fassara
Harsuna Sudanese Arabic (en) Fassara
Turanci
Sana'a
Sana'a Malami da Farfesa
Wurin aiki Jami'ar Khartoum da King Saud University (en) Fassara
Employers Jami'ar Khartoum
UNESCO
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Salih a Wad Madani, Sudan a shekara ta (1944) [upper-alpha 1] Salih ya shiga Jami'ar Khartoum a shekarar 1963 kuma ya sami digiri na farko a fannin Kimiyya tare da Daraja ta Farko a Injiniya na Jama'a a shekarar (1969) Daga nan ya sami Diploma na Kwalejin Imperial kuma ya ci gaba da kammala digirin digirgir a cikin Hydraulics a shekarar (1972) daga Kwalejin Imperial London. Daga baya ya sami Diploma a fannin Hydrology daga Jami'ar Padua, Italiya, a shekarar (1974).[4] [5]

Bincike da aiki

gyara sashe

Bayan kammala karatun digirin digirgir, Salih ya koma ƙasar Sudan a shekarar 1973, ya shiga Kwalejin Injiniya ta Jami’ar Khartoum a matsayin malami kafin ya zama mataimakin farfesa a shekarar (1977) shugaban sashen injiniyanci a shekarar 1979, kuma cikakken farfesa ne a shekarar 1982. Ya zama Mataimakin Shugaban Jami'ar Khartoum tsakanin shekarun (1990) zuwa (1991). Tun daga watan Nuwamba 2022, shi malami ne a Sashen Injiniya na Jama'a, a Jami'ar Khartoum, kuma memba a Majalisar Gudanarwa na Jami'ar Khartoum da Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Sudan. Har ila yau, Farfesa ne a Kwalejin Injiniyanci, Jami'ar Sarki Saud, daga shekarun (1982) har zuwa.[6]

Aikin bincike da tuntuba Salih ya maida hankali ne kan tsaron ruwa da kula da albarkatun ruwa. Ya yi aiki a UNESCO daga shekara ta 1993 har ya zama Darakta na Sashen Kimiyyar Ruwa a shekarar 2011, [7] kuma ya kasance memba a Hukumar Zartarwa ta UNESCO daga shekarun 2015 har zuwa 2019.[8] Ya kuma kasance mataimakin Gwamnan Majalisar Ruwa ta Duniya tsakanin shekarun (1999) zuwa 2003. Salih yana aiki a matsayin mai ba da shawara ga babban hukumar raya birnin Riyadh, Saudi Arabia, shi memba ne na yawancin kungiyoyin ruwa na duniya, kuma ya kasance memba na juri na yawancin kyaututtukan ruwa na duniya.[9]

Kyaututtuka da karramawa

gyara sashe

An zabi Salih a matsayin Fellow na Ƙungiyar Albarkatun Ruwa ta Duniya (FIWRA) a cikin shekarar (1983), Fellow of the African Academy of Sciences (FAAS) a shekarar (1993),[10] kuma Fellow of the Word Academy of Sciences. (FTWAS) a cikin shekarar 2002.[11]

Ya samu lambar yabo ta kungiyar Islamic World Educational, Science and Cultural Organisation (ISESCO) don kwarewa a fannin bincike na kimiyya.

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Salih yana da aure da ‘ya’ya uku.

wallafe-wallafen da aka zaɓa

gyara sashe

Duba kuma

gyara sashe
  • Elfatih Eltahir
  • Yahia Abdel Mageed

Manazarta

gyara sashe
  1. "Abdin Mohamed Ali Salih | Just another UofK site" . Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  2. "Salih Abdin Mohamed Ali | The AAS" . www.aasciences.africa . Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  3. iAgua, redaccion (2011-10-05). "Abdin Mohamed Ali Salih, nuevo Director para la División de Ciencias del Agua y Secretario del PHI de la UNESCO" . iAgua (in Spanish). Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  4. " ﺑﺮﻭﻓﺴﻮﺭ ﻋﺎﺑﺪﻳﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﻋﻠﻰ ﺻﺎﻟﺢ ﺑﻘﻠﻢ ﺑﺨﻴﺘﺔ ﺍﻣﻴﻦ " . danagla.ahlamontada.com (in Arabic). Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  5. "CV" (PDF). Archived (PDF) from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  6. "Cssp" . www.bibalex.org . Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  7. "Side Event at the ICSU Forum on Science, Technology and Innovation // "Water security" A New Paradigm of Adaptive Management | Nexus - The Water, Energy & Food Security Resource Platform" . www.water-energy-food.org . Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  8. "Wagner elected as new Chair of UNESCO- IHE" . Diplomat magazine . 2015-12-05. Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  9. Stephenson, David (2005). Water services management / { Prof. Abdin Mohamed Ali Salih collection } . London: Lightning Source UK Ltd. ISBN 978-1-84339-080-0
  10. "Abdin Mohamed Ali Salih's biography, net worth, fact, career, awards and life story - ZGR.net" . www.zgr.net . Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.
  11. "Salih, Abdin Mohamed Ali" . TWAS . Archived from the original on 2022-11-13. Retrieved 2022-11-13.