Abderraouf El Basti ɗan siyasan Tunusiya ne. Shi ne tsohon Ministan Al'adu da Kariya na Kayan Tarihi a kasar Tunusiya.

Abderraouf El Basti
Minister of Culture (en) Fassara

29 ga Augusta, 2008 - 14 ga Janairu, 2011
shugaba

1979 - 1981
Rayuwa
Haihuwa Tunis, 19 ga Augusta, 1947 (77 shekaru)
ƙasa French protectorate of Tunisia (en) Fassara
Tunisiya
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Makaranta Sadiki College (en) Fassara
Tunis University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya

Tarihin rayuwa

gyara sashe

An haifi Abderraouf El Basti a ranar 19 ga watan Agustan shekarar 1947. [1] Ya sami digiri na biyu a adabin larabci daga Jami’ar Tunis .

 
Abderraouf El Basti

Daga shekarar 1981 zuwa 1988, ya yi aiki da Union des Radios Arabes, kuma shi ne Shugabanta daga shekarar 1989 zuwa 1998. [1] Daga 1999 zuwa 2000, ya kasance Jakadan Tunusiya a Lebanon . Daga 2000 zuwa 2002, ya kasance Shugaban Établissement de la Radiodiffusion-Télévision Tunisienne . Ya kasance Ambasada a Jordan . A 2007, an nada shi a matsayin Sakataren Harkokin Waje na Ma’aikatar Harkokin Waje . A shekarar 2008, ya zama Ministan Al'adu da Kariya na Al'adun Gargajiya.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Business News