Abacha birni ne, da ke a jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya. Birnin ya yi iyaka da garuruwan Abatete, Nimo, Oraukwu da Eziowelle. Haka-zalika ya na ɗaya daga cikin al'ummomi goma da ke karamar hukumar Idemili North a jihar Anambra, sannan kuma ya na a cikin shiyyar Sanatan Anambra ta tsakiya. Al’ummarta na cikin al’ummomin da ke magana da harshen Igbo a yankin da ke gabashin Najeriya. Garin Abacha ya ƙunshi ƙauyuka biyar da hukuma ta tabbatar; Umudisi, Umuazu, Umuokpolonwu, Umuekpeli, da Ugwuma, tare da 'yan uwan Nogba da suke burin zama ƙauyen nasu. Kauyen Umuokpolonwu na Abacha yana da kauyuka biyu, wato: Umunneora dakuma Umuaribo.

Abacha

Wuri
Map
 6°08′36″N 6°57′25″E / 6.14321°N 6.95695°E / 6.14321; 6.95695
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Anambra
Abacha
 

An naɗa Cif Nwabunwanne Godwin Odiegwu sarautar Ezedioramma Ikendim Abachaleku III, Igwe (Sarkin) na Abacha a ranar 9 ga Janairu, 2021,[1][2] bayan da gwamnatin Willie Obiano ta tuɓe wanda ya gabace shi, Igwe Godwin Chuba Mbakwe, duk da cewa har yanzu lamarin yana nan daram. kotun da ke da hurumin tantance halascin ko akasin abin da gwamnatin Willie Obiano ta yi; Ndi Anambra ya ayyana shi a matsayin gwamnan da ya fi kowa aiki bayan Chinwoke Mbadinuju, sannan kuma gwamnan jihar Anambra Willie Obiano ya janye takardar shaidarsa a matsayin Igwe a watan Disambar 2020.[3][4]

Manazarta

gyara sashe
  1. Thompson, Enitan (2021-08-15). "Igwe Odiegwu Of Abacha Community Idemili North Council Area Celebrates First Iwa Ji Festival". TDPel Media (in Turanci). Archived from the original on 2021-11-29. Retrieved 2021-11-29.
  2. "Abacha Development Union In North America Honours New Traditional Ruler Igwe Odiegwu, Traditional Prime Minister Omofia". Heartbeat Of The East (in Turanci). Retrieved 2021-11-29.
  3. "Another Anambra community disowns suspended Monarch over Abuja trip". Vanguard News (in Turanci). 2020-08-25. Retrieved 2021-11-29.
  4. "Anambra community boils over plot to appoint acting Igwe". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-11-01. Archived from the original on 2021-11-29. Retrieved 2021-11-29.