Ƙungiyar Littafi Mai-Tsarki ta Najeriya
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Bible Society of Nigeria ( BSN ) kungiya ce mai zaman kanta ta Kirista ba don samun riba ba a Najeriya wacce ke fassara, bugawa da rarraba Littafi Mai-Tsarki na Bayibul a harshen Turanci dama wasu harsunan Najeriya da yawa.[1][2][3][4] An kafa kungiyar a ranar 8 ga watan Fabrairu 1966, an gina ƙungiyar a kan aikin farko na Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki ta Birtaniya da Ƙasashen waje, Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki ta Amirka, da Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki ta Scotland, waɗanda suka fassara kuma suka buga Littafi Mai-Tsarki na Bayibul a cikin harshen Efik a shekarar 1868.[5] Fasto Samuel Adesola Sanusi shine babban sakatare kuma babban jami'in ƙungiyar Bible Society of Nigeria a yanzu.
Ƙungiyar Littafi Mai-Tsarki ta Najeriya | |
---|---|
Founded | 1966 |
Classification |
|
Tarihi
gyara sasheAn kafa kungiyar Bible Society of Nigeria, ranar 8 ga Fabrairun 1966 ta hanyar ƙoƙarin farko na Marigayi Dr. Francis Ezeogo Akanu Ibiam, ɗan asalin yankin na farko na rusasshiyar yankin Gabas. Tun da farko a watan Fabrairu, 1965, Dokta Ibiam ya fara tuntuɓar wakilan yawancin Coci [Kungiyoyin Majami'u) a Najeriya kan buƙatar kafa ƙungiyar Littafi Mai Tsarki na Bayibul ta ƙasa a Najeriya. An yanke shawara gaba ɗaya na waccan taron ne aka kafa kungiyar Bible Society of Nigeria wanda sakamakon haka ya kai ga kafa gami da kaddamar da ita a ranar 8 ga watan Fabrairu 1966. Kafin 1966, Ƙungiyar tana ƙarƙashin kulawar Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki na Bayibul ta Biritaniya da Ƙasashen Waje [BFBS] wadda ta yi aiki a Najeriya tun daga 1807. Sai kuma Littafi Mai Tsarki House, Apapa yana hidima a matsayin cibiyar rarraba wa wasu ƙasashe na Yammacin maƙwabtan Afirka.
Al'umma A Yau
gyara sasheAl'ummar wannan ƙungiya na da hedkwatarta a Office Address 18, Wharf Road, Apapa, Jihar Legas, Najeriya. Ofishin kamfani yana a lamba 150, Ikorodu Road, Onipanu, Jihar Legas, Najeriya. Tana da cibiyoyin rarraba Littafin Mai Tsarki na Bayibul a wasu garuruwan Najeriya:
- ABUJA: 23, Ndola Crescent, Wuse Zone 5, Abuja.
- LAGOS II: 7, Boladale Street, Opposite Mr. Biggs Oshodi.
- ABA: The Bible Society of Nigeria, St. Michael’s Cathedral, St. Michael’s Road, Aba.
- JOS: The Bible Society of Nigeria, 53, Tafawa Balewa Road, Jos.
- IBADAN: Plot 7A, Trinity Avenue, Educational Estate Samonda, Ibadan.[6]
Ayyukan Fassara
gyara sasheKungiyar ta fassara Littafi Mai Tsarki na Bayibul, zuwa harsuna 26 na Najeriya.[7][8]
Daga cikin harsuna ashirin da shida (26) da aka fassara Littafin Mai Tsarki na Bayibul sun haɗa da:
- Kalabari,
- Okrika,
- Isoko,
- Igala,
- Igede,
- Ebira,
- Yoruba,
- Efik,
- Igbo,
- Hausa,
- Nupe,
- Khana,
- Urhobo,
- Fulfude,
- Bokyi,
- Edo,
- Tiv,
Bura
Gidajen Baƙi
gyara sasheƘungiyar Littafi Mai Tsarki na Bayibul ta Najeriya na da gidajen baƙi uku da ke a cikin biranen Najeriya uku ( Lagos, Ibadan da babban birnin tarayyar Abuja ). [11]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Abiaziem, Chinyere. "BSN Marks Bible Week, Seeks Prayers For Nigeria". Independent. Ogba, Ikeja, Nigeria. Retrieved 31 May 2018.
- ↑ "Bible Society of Nigeria's board meeting". Punch. Nigeria. 18 April 2018. Retrieved 31 May 2018.
- ↑ "The Light from Zion Shines over Nigeria". Breaking Israel News. Retrieved 31 May 2018.
- ↑ "What we do". biblesociety-nigeria.org. Bible Society of Nigeria.
- ↑ "BSN @ 52: Nigeria would have been on fire if…. —Ajiboye". Vanguard. 11 March 2018.
- ↑ "Contact Us". Bible Society of Nigeria (in Turanci). 2015-12-28. Retrieved 2019-11-01.
- ↑ Latona, Olayinka (1 April 2018). "BSN unveils Kalabari, Okrika bibles". Vanguard News. Retrieved 2 February 2019.
- ↑ "We secure Nigerian languages through Bible translation — BSN boss". Vanguard News (in Turanci). 2016-01-23. Retrieved 2019-11-01.
- ↑ "BSN Completes Translation of Bible in 24 Nigerian Languages". THISDAYLIVE (in Turanci). 2016-09-05. Retrieved 2019-11-01.
- ↑ "Bible now in 24 Nigerian languages". The Sun Nigeria (in Turanci). 2016-09-05. Retrieved 2019-11-01.
- ↑ "About Us – Bible Guest House – Research and Development Center" (in Turanci). Archived from the original on 2019-11-01. Retrieved 2019-11-01.