Ƙungiyar Ɗalibai da Matasa ta Duniya
Ƙungiyar dalibai da Matasa ta Duniya (WOSY) ƙungiya ce ta ɗalibai da matasa ta duniya baki ɗaya, tare da ƙasar Indiya a matsayin hedkwatar. An kafa ta a jihar Delhi a ranar ashirin da tara 29 ga Oktoban shekara ta dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985. A halin yanzu, Mista Nitin Sharma shi ne Shugaban WOSY. Mista Sharma yana aiki ne ga wani kamfani na ƙasar Switzerland. Har ila yau, shi ne mai kula da ƙasa da ƙasashen na ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam a ƙarƙashin ƙungiyar Civil Societies 20 India . Mista Shubham Goyal shine Babban Sakataren WOSY. Shubham, mai ba da shawara ne a Babban Kotun Delhi a wannan Kasa tasu.
Ƙungiyar Ɗalibai da Matasa ta Duniya | |
---|---|
Bayanai | |
Farawa | 1985 |
Shafin yanar gizo | wosy.org |
Tarihi
gyara sasheAn ƙaddamar da Ƙungiyar Ɗalibai da Matasa ta Duniyane a Delhi a ranar ashirin da tara 29 ga Oktoban shekarar dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985 a lokacin Taron Shekarar Matasa ta Duniya a tsakiyar wakilai dubu goma sha daya 11,000 na ɗalibai daga ƙasashe goma sha huɗu. Atal Bihari Vajpayee, wanda zai zama Firayim Minista bayan ya samu nasarar tsayawa takara a Babban Zaɓe na ƙasar Indiya na shekarar dubu daya da dari tara da chassa'in da shidda 1996, ya ƙaddamar da ƙungiyar. Air Chief Marshal Arjan Singh na Sojojin Sama dake a Indiya da Swami Ranganathananda, shugaban na goma sha uku 13 na Ramakrishna Math da Ramakrishn Mission, sun halarci taron buɗewa.
Manufofin
gyara sashe- Fahimtar kasa da kasa da hadin kai tare da kusanci na "Duniya Iyali ce"
- Yada manufofin Majalisar Dinkin Duniya na zaman lafiya da haɗin kai.
- Haɗakar da ɗalibai da matasa na duniya tare don inganta adalci na zamantakewa da bil'adama.
- Taimaka wa motsi na ɗalibai da matasa don ba da damar hulɗar al'adu, bayanai, ilimi da hikima a duniya.
- Samar da dalibai da ra'ayin matasa da shirya su don yaki da ta'addanci, tsattsauran ra'ayi na addini, wariyar launin fatawariyar launin fata" data-linkid="35" href="./Colonialism" id="mwJA" rel="mw:WikiLink" title="Colonialism">mulkin mallaka, wariyar jinsi, mulkin mallakar da zalunci na kowane irin.
- Yaɗa bil'adama da ruhaniya wanda, haɗe da hangen nesa na kimiyya, na iya ba da falsafar rayuwa mai yiwuwa ga duniya.
Ƙungiyoyin da ke da alaƙa
gyara sashe- Pragyik Vidyarthi Parishad, Nepal
- Taron Dalibai na Kasa, Burtaniya
- Taron Matasan Tibet, Dharmashala, Indiya
- Taron Kasa na Tibet, Dharmashala, Indiya
- Abokan Tibet, Dharmashala, Indiya
- Taron Kasa, Afirka ta Kudu
- Ƙungiyar Matasa da Dalibai ta Najeriya (NYSO) Najeriya
- Akhil Bharatiya Vidyarthi Parishad, Indiya
Duba kuma
gyara sashe- Shirin Matasa na Duniya
- Ƙungiyar ɗalibai
Bayanan da aka ambata
gyara sashe- "WOSY(World Organisation of Student and Youth)". ABVP Orissa. Archived from the original on 12 October 2009.
- "WOSY Bangalore". Archived from the original on 10 January 2011.
- "Two-day international convention of WOSY". Archived from the original on 6 October 2008. Retrieved 6 January 2010.