Kudan Tsando, wanda a turance ake kira da Tse-tse fly, wasu manyan kudaje ne masu cizo da akafi samunsu a wurare na zafi a yankin nahiyar Afirka. Waɗanda ke rayuwa ta hanyar shan jinin dabbobi.

kudan Tsando

Nazari gyara sashe

An yi nazari sosai kan kudan tsando saboda rawar da suke takawa wajen yada cututtuka.[1] Suna da babban tasiri na tattalin arziki a yankin kudu da hamadar sahara a matsayin abubuwan da ke haifar da kwayar cutar trypanosomes, wadda ke haifar da cututtukan bacci da na dabbobi. Yawanci suna haifar da 'ya'ya huɗu a kowace shekara, a tsawon rayuwarsu.

Manazarta gyara sashe