Ƙauyen Gubana
Gubana ƙauye ne da ke cikin ƙaramar hukumar Fune ta jihar yobe a Najeriya.
Tarihi
gyara sasheGubana ƙauye ne da ke cikin ƙaramar hukumar Fune ta jihar Yobe a Najeriya ya kasance ƙauye ne wanda ya kai shekara dari biyu da ashirin da biyar 225 da kafuwa a wancan lokacin Bazemfila mahaifin sarki bah, ya yi ƙaura daga Mai wala zuwa Mai dala, da aka fi sani da (Gubana) tare da ɗansa a dalilin sarkin Mai wala yana alfahari a kullum babu wani mutum kamarsa ko sama da shi a kauyen Mai wala dole ne kowa ya kasance a karkashinsa irin wadannan kalaman sun yi rauni a zuciyar Bazemfila ya yanke shawarar canza wurin zama, da ya yi hijira daga Mai wala, zuwa Maidala. Maidala abokin Bazemfila ne kuma Bazemfila ya fi Mai dala arziki a kauyen, Bazemfila ya rasu ya bar dansa mai suna bah kafin Bazemfila ya mutu yana rike da sarautar Gubana a matsayin sarki domin shi ne mafi karfin hali kuma attajiri.[1]
Mulki
gyara sasheMasarautar bah ta fara daga shekara ta alif 1880, zuwa shekara ta alif 1930, sarki, ya yi aure kuma ya haifi ‘ya’yansa tagwaye mace da namiji, an haife su a shekarar ta alif 1891, sunan namijin Yerima Ussaini, Yerima haifaffen Gubana ne, kuma ya karbi Masarautar mahaifinsa daga shekara ta alif 1930, zuwa shekara ta alif 1970. A shekara ta alif 1970, Ussaini (Barde) ya yanke shawarar yin aikin hajji a shekara ta alif 1970, ya tafi aikin hajji ya bar wa dansa Yerima Ibrahim Ussaini Barde sarauta bayan ya koma gida ya ki karbar mulkinsa daga Yerima, a shekara ta alif 1970, Yerima Ibrahim ya zama sarkin Gubana. Sarki Barde ya rasu a shekarar ta alif 1996, ya yi shekara dari da biyar 105 da shekara arba'in 40 a matsayin sarki, kafin ya rasu ya bar ‘ya’ya 14 mata 6 da maza 8. Ya zuwa yanzu sarki Ibrahim Ussaini Barde shine sarkin Gubana yana da shekaru 96 a duniya, dansa Yerima idriss Ibrahim Barde ne yake wakilce shi a masarauta domin ya riga ya tsufa, Yerima ya fara gudanar da sarautar a shekarar dubu biyu da goma shabiyar 2015 zuwa yau.[2] akwai asibti a kauyen.[3]
Arziki
gyara sasheGubana ƙauyen ne da ke da mashahuri sosai waɗanda suka dace da noman dawa da wake.
Ilimi
gyara sasheGubana tana da ilimi na Musulunci da na zamani suna yin karatun Islama a cikin nau'in gargajiya da ake kira Tsangaya. Kuma yawanci ana amfani da su (warash), a ilimin zamani suna da ilimin firamare wanda ya yi sama da shekaru 35 a ƙauyen.
Addini
gyara sasheDuk Gubana musulmi ne kuma kashi 85% na warash ne, yayinda sauran suke amfani da sunni. Masana'antu a farkon Gubana suna da sana'ar gargajiya kamar samar da farcen gatari wasu kuma aski na gargajiya, da kiwon dabbobi.
Iyaka
gyara sasheGubana yana da iyaka da ƙauyuka a yammacin Maiwala, gabas Gubanan dutse, arewa kuma shine Ngubdo.
Manazarta
gyara sashe- ↑ http://www.maplandia.com/nigeria/yobe/fune/gurbana/gurbana-google-earth.html
- ↑ https://dailytrust.com/tags/idi-barde-guban[permanent dead link]
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-16. Retrieved 2022-01-16.