Ƙamus turanci dictionary, kuma akan kira shi da suna littafin kalmomi, kundi ne na tarin kalmomi a Jere, a cikin harshe ko harsuna daban-daban, ana kuma jera kalmomin ne a tsarin zuwan baƙaƙe, ƙamus na dauke da bayanai na ma'anoni, anfani, etymologies, furucci, fassarori, na kalmomin dake cikin harshe da sauran su.[1] ko kuma ƙamus kan zama wani littafi ne dake ƙunshe da kalmomin dake cikin wata harshe da kuma irin su daga wata harshen, wanda ake kira da turanci lexicon.[1] It is a lexicographical reference that shows inter-relationships among the data.[2]

ƙamus
book form (en) Fassara da literary genre (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na knowledge organization system (en) Fassara, literary work (en) Fassara, lexicographic work (en) Fassara, publication (en) Fassara da Manazarta
Tarihin maudu'i Q3137844 Fassara
Manifestation of (en) Fassara terminology (en) Fassara
Entry in abbreviations table (en) Fassara слов.
ƙamus na Turanci-zuwa Turanci da Turanci-zuwa Farsi
Babban Ƙamus na Latin daga Egidio Forcellini.
ƙamus na Langenscheidt

Akwai babban muhimmin banbanci da akayi tsakanin ƙamus na gama gari wanda ake kira da general da kuma ƙamus mai muhimmanci wato specialized dictionary. Shi ƙamus mai muhimmanci yana ɗauke ne da kalmomi da suka keɓanci wani fanni na ilimi kawai, bawai yana ɗauke da dukkanin kalmomin harshe bane. Su kuma kalman da ake amfani da su wurin fayyace kowane ma'ana na kalmomin ana kiran sune da suna terms bawai kalmomi ba wato words.[3] Har wayau akwai wasu nau'ukan ƙamus, waɗanda ke da tsarin su daban, misali, ƙamus mai harsuna biyu bilingual (translation) dictionary, ƙamus mai bada ma'anoni iri ɗaya dictionary of synonym (thesaurus), da kuma ƙamus da ake kira rhyming dictionary da turanci.[4]

Akwai kuma banbanci tsakanin ƙamus prescriptive da descriptive; na farkon na nufin yin bayani akan abunda ake gani shine ingantacce a wurin amfani da harshe inda na biyun ke nufin yin bayani akan abunda shine ake amfani da kalmomi da su zahiri.[5]

An samu cewa farkon samun amfani da ƙamus ya faro run a lokacin Sumer, amma yawan cin ƙamus ɗin lokacin na ma'anar harsuna ne, (wato bilingual dictionaries).[4][6]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 Webster's New World College Dictionary, Fourth Edition, 2002
  2. Nielsen, Sandro (2008). "The Effect of Lexicographical Information Costs on Dictionary Naming and Use". Lexikos. 18: 170–189. ISSN 1684-4904.
  3. A Practical Guide to Lexicography, Sterkenburg 2003, pp. 155–157
  4. 4.0 4.1 A Practical Guide to Lexicography, Sterkenburg 2003, pp. 3–4
  5. A Practical Guide to Lexicography, Sterkenburg 2003, p. 7
  6. R. R. K. Hartmann (2003). Lexicography: Dictionaries, compilers, critics, and users. Routledge. p. 21. ISBN 978-0-415-25366-6.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.