Ɗinya Ana kiranta da turanci (Black plump) wata bishiya ce mai ƴa'ƴa, kafin su nuna kalansu ruwan ganye ne kore (green) bayan kuma ta nuna sai su ƙoma baƙaƙe. Tana fitowa a daji ko a gonaki haka kuma tana girma sosai, amma tana fara yin ɗiya tun bata gama girma ba. Ana kuma cin ganyen ta a lokacin da yake sabon toho, sai a ɗiboshi a dafa bayan an dafa sai a gyara shi ta yadda ɗacin shi zai gushe, daga nan sai a kwaɗa da ƙuli-ƙuli da albasa da sauran kayan haɗin, wannan shine ake kira da (ɗinkin). Ɗinya tana maganin mura, tari, asma da kuma garkuwa jiki.[1] Ana shan ƴaƴanta sosai kuma tanada amfani sosai a jikin Dan Adam.[2]

Ɗinya
Conservation status

Least Concern (en) Fassara  (IUCN 3.1)
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderRosales (en) Rosales
DangiRosaceae (en) Rosaceae
TribeAmygdaleae (en) Amygdaleae
GenusPrunus (en) Prunus
jinsi Prunus nigra
Aiton,
Geographic distribution
Ya-yan dinya

Manazarta gyara sashe

  1. Saddiq, Mustapha (3 August 2018). "Anfani 5 da 'ya'yan iccen dinya keyi a rayuwar bil'adama". legit hausa. Retrieved 29 June 2021.
  2. A Hunkuyi, Umar (6 April 2019). "Amfanin 'Ya'yan Itacen Dinya A Jikin Dan'adam". leadership Ayau. Retrieved 29 June 2021.