Ɓirchi
Ɓirchi ana kiran sarautar Birchi da suna “mai garin ɓirchi” kuma da haka ake kiran kowane shugaban wannan masarautar dashi. An kafa garin ɓirchi da dadewa tun zamanin maguzawan hausawa, Sannan kuma tsantsar hausawa suka kafa garin ɓirchi kuma ana ma garin kirari da “kainafara arnan Ɓirchi[1] Garin Ɓirchi ya samo sunansa daga shugaban farko na maguzawa “kainafara” wanda ake kira da Ɓirchi wanda ya fito ne daga garin Misra[1].
Tarihi
gyara sasheGarin Ɓirchi tana zagaye da garuruwa kamar haka: rawayau, ta ɓangaren gabas, kuma garin wurma ta ɓangaren yamma, ta ɓangaren arewa, birnin agga, ta kudu kuwa tana makwabtaka da garin dabawa[1]. Ɓirchi nada ganuwa mai cikakkiyar kariya sannan har yanzu akwai “dutsen ɗan talle” wanda mutanen farko wato maguzawa ke zuwa domin ayyukan bauta[1].
Cigaba
gyara sasheAn samar da makarantun zamani na farko na garin ɓirchi a zamanin ɓirchi Muhammadu (1937 – 1955 ) kuma yayi iya kokarin sa wajen jawo hankalin iyaye bisa ‘yayansu suyi karatu kuma ya samar wa manoma tallafi musamman kayan aikin gona[2]. An sama bunƙasar noma a lokacin rabi’u ɓirchi a shekarar (1907 – 1937) wanda ya hau kan mulki kuma ya kawar da matsalar yunwa na lokacin wanda ake kira “yunwar kwana”[2].Daga cikin kayan tarihin Birchi da basu gushe ba akwai marinu da kayan aikin rini wanda har yanzu ana anfani dasu[2] Daga cikin wadanda suka mulki garin Ɓirchi na kurkusa sun haɗa da[3]:
Sarakuna
gyara sashe- Mai gari Ɓirchi, kunkuru.
- Mai gari Ɓirchi, alu
- Mai gari Ɓirchii Zubairu.
- Mai gari Ɓirchi, Kiɗe.
- Mai gari Ɓirchi Rabi’u. (1907 – 1937)
- Mai gari Ɓirchi Muhammadu (1937 – 1955)
- Mai gari Ɓirchi Abdulqadir (1968)[3].
Bibiliyo
gyara sashe- Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.14. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.15. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ 3.0 3.1 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.16. ISBN 978-2105-93-7.