Youssouf Togoïmi (an haifeshi ranar 26 ga watan Maris, 1953 - ya mutu ranar 24 ga Satumban shekarar ta 2002 ) ɗan siyasan ƙasar Chadi ne wanda ya yi aiki a cikin gwamnati a ƙarƙashin Shugaba Idriss Déby amma daga baya ya jagoranci wata ƙungiyar tawaye, the Movement for Democracy and Justice in Chad (MDJT), a kan Déby.

Youssouf Togoïmi
Rayuwa
Haihuwa 26 ga Maris, 1953
ƙasa Cadi
Mutuwa 24 Satumba 2002
Karatu
Harsuna Larabci
Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwa da Aiki

gyara sashe

An haife shi a garin Zouar a cikin tsaunukan Tibesti, ya fito ne daga arewacin musulmin ƙasar. Togoïmi ya yi aiki a mukamai da yawa a lokacin shugabancin Idriss Déby: ya kasance Ministan Shari'a daga shekarar 1990 zuwa 1993, Ministan Tsaro daga shekarar 1995 zuwa 1997, sannan kuma aka nada shi Ministan cikin gida a ranar 21 ga Mayun 1997.[1] Jim kaɗan bayan nadin na ƙarshe, ya yi murabus daga mukaminsa na gwamnati a ranar 3 ga watan Yunin 1997. Ya ce murabus din nasa ya samo asali ne saboda abin da ya bayyana da "mulkin kama-karya" ta gwamnati. Hakanan an fassara barin aikin da Togoïmi yayi da Déby a matsayin abin da ke da alaƙa da ƙabilanci dangane da kasantuwar sa ɗan ƙabilar Toubou shi kuma Déby ɗan ƙabilar Zaghawa.

Manazarta

gyara sashe
  1. "May 1997 – New Attack", Keesing's Record of World Events, volume 43, May 1997, page 41,626.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe