Yau Usman Idris kwararren masanin kimiyyar nukiliyar Najeriya ne kuma shine babban darekta na yanzu a Hukumar Kula da Nuclear ta Najeriya (NNRA).[1][2]Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi.[3][4][5]

Yau Usman Idris
Rayuwa
Haihuwa Kauru
Sana'a

Farkon rayuwa da ilimi

gyara sashe

An haife Idris a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna. Ya samu Digirinsa na B.sc a Jami’ar Maiduguri a (1988), M.sc. Physics a Jami’ar Ibadan a (1992), da P.hD. Fannin kimiyyar nukiliya a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a (1998).[2]

Farkon tashe

gyara sashe

Idris ya yi aiki a wurare daban-daban a fannin makamashin nukiliya kuma yanzu shi ne darekta janar na Hukumar Kula da Nuclear ta Najeriya (NNRA). Gwamnatin jihar Kaduna ta nada shi kwamishinan muhalli da albarkatun kasa.[6]

Kwarewar Nuclear

gyara sashe

Shi ne mataimakin shugaban kungiyar kula da fasahar nukiliya ta Afirka (FNRA)

Babban mai kula da yankin Afirka na Hukumar Makamashi na Kasa da Kasa (IAEA)

Memba a kwamitin ba da shawara, Kungiyar Kasuwancin Nuclear Afirka.[2]

Rayuwar kashin kai

gyara sashe

Ya yi aure yana da yara.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://en.m.wikipedia.org/wiki/Yau_Usman_Idris#cite_note-4
  2. 2.0 2.1 2.2 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-09-25. Retrieved 2020-08-23.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-06-20. Retrieved 2020-08-23.
  4. https://newswirengr.com/2020/05/29/yau-usman-idris-appointed-as-dg-of-nigeria-nuclear-regulatory-authority/
  5. https://www.thisdaylive.com/index.php/2020/05/28/buhari-appoints-idris-head-of-nigerias-nuclear-regulatory-body/
  6. https://en.m.wikipedia.org/wiki/Yau_Usman_Idris#cite_note-11